✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakeem Baba-Ahmed: Kakakin Dattawan Arewa ya koma PRP

Ya ce ya shiga PRP ne saboda manyan jam'iyyu sun sa Najeriya a tsaka mai wuya.

Kakakin Kungiyar Dattawan Arewa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya yanki tikitin jam’iyyar PRP.

Hakeem Baba-Ahmed wanda ke cikin wadanda suka yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yakin neman zabe a 2015 ya sanar da haka ne a ranar Alhamis.

“Na yanki katin shiga jam’iyyar PRP da kyakykyawar niyya. Ina rokon Allah Ya taimake ni da sauran ’yan uwa masu tsoron Allah da niyyar fidda Arewa da Najeriya daga cikin halin da manyan jam’iyyun siyasa suka jefa mu.

“In sha Allah za mu yi nasarar karfafa adalci da rikon amana da taimakon talaka a Najeriya,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Hakeem Baba-Ahmed, ya sha caccakar gwamnatin Shugaba Buhari kan gazawarta wajen samar da tsaro da sauran matsalolin da ya ce suna barazana ga dorewar Najeriya daga yanzu zuwa shekarar 2023.

Aminiya ta kawo muku tattaunawar da ta yi da shi inda a ciki ya yi nadamar zaben tumun dare da suka sa ’yan Najeriya suka yi wajen zaben Shugaba Buhari.

A cewarsa, sun yi wa Buhari yakin neman zabe da kyakkyawan niyyar cewa zai fitar da ’yan Najeriya dag mawuyacin halin da kasar ta shiga a baya, amma Buharin ya watsa musu kasa a ido, domin ya ma fi magabacinshi gazawa.

A zantawar, Kakakin na dattawan Arewa ya kuma zargi jamiyyun APC da PDP da rashin sanin abin da ya kamata su yi domin fitar da Najeriya daga halin tsaka mai wuya da ta tsinci kanta a ciki.

APC da PDP duk uwarsu daya, sun lalace, wannan tana mulki… Tana nan tana kacaniya. PDP kuma tana hammaya, amma hamayyar da suke wa junansu ma ya fi wanda suke wa gwamnati. Wai kuma wadannan su ne, wannan tana so ta ci gaba, wannan kuma tana son ta kwace mulki daga hannunta.”