✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakikanin abin da ya kai Jonathan wurin Buhari

Jami'ai sun ce rikicin Mali aka tattauna, amma wasu manazarta na ganin akwai lauje cikin nadi

Ziyarar da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya kai Fadar Shugaban Kasa ta Aso Villa, inda ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu a cikin ‘yan kwanaki, ta jawo ce-ce-ku-ce.

A cewar Femi Adesina, Babban Mai Bayar da Shawara ga Shugaban Kasa a kan al’amuran yada labarai, shugabannin biyu sun tattauna ne a kan kasar Mali.

Ya kara da cewa akwai wani taron ECOWAS na musamman da za a gudanar a Ghana ranar Lahadi game da rikicin kasar ta Mali.

Don haka ne, inji shi, Mista Jonathan ya je ya yi wa Buhari bayani.

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan ne dai Wakilin ECOWAS na Musamman mai shiga tsakanin don sasanta rikicin Mali.

Lauje cikin nadi?

Sai dai kuma wasu manazarta na ganin cewa wannan bayani ba komai ba ne illa fakewa da guzuma a harbi karsana.

A ganin masu irin wannan ra’ayi, siyasar 2023 ce kadai za ta kai Mista Jonathan wurin Shugaba Buhari sau biyu a cikin dan kankanin lokaci.

Idan maganar Mali ce, a wannan mahangar, ai sai shugabannin biyu su yi magana ta waya.

Ma’ana bukatar tattaunawa cikin sirri ba tare da yiwuwar wani ya ji ba ce kawai za ta sanya Jonathan jele zuwa Fadar Shugaban Kasa.

Ana dasawa

Mai yiwuwa dai masu irin wannan ra’ayi suna la’akari ne da yadda shugabannin biyu ke dasawa duk da cewa daya ya kayar da dayan a zabe.

Babu shakka akwai masu ganin cewa a Najeriya ba a taba samun shugaban kasa mai ci yana dasawa da tsohon shugaban kasa kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke yi da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ba.

Ko da yake tun bayan da Jonathan ya amince da kaye a zaben 2015 ba tare da kai ruwa rana ba Buhari ya bayyana shi a matsayin mutum mai dattako, yake kuma yabon shi.

Bugu da kari, duk shekara Buhari kan yi amfani da dadadan kalamai wajen siffanta Mista Jonathn a duk lokacin da ranar haihuwarsa ta zagayo.

Sannan kuma tun farkon shigar Shugaba Buhari Fadar Shugaban Kasa wasu magoya baya da makusantan Mista Jonathan suke sukar gwamnatirsa.

Amma wani nazari ya nuna cewa a ’yan kwanakin nan masu sukar ko dai sun rage matuka, ko kuma sun daina gaba daya.

A hirarsa da gidan talabijin na Channels ranar Laraba, Shugaba Buhari ya ce bai damu da wanda zai gaje shi ba idan ya kammala wa’adin mulkinsa ya sauka.

Ma’ana ba zai nuna goyon baya ko ya tsaya wa wani don a zabe shi a matsayin shugaban kasa ba.

Sai dai wasu na ganin akwai wata a kasa, musamman idan aka yi la’akari da kalamansa cewa idan ya ambaci sunan wanda yake sha’awa ya gaje shi, zai jawo mishi jangwam.

Sauya sheka zuwa APC

Da ma dai an dade ana rade-radin cewa Mista Jonathan zai sauya sheka.

Idan mai karatu bai manta ba, a watan Nuwamba na shekarar 2020 gwamnonin APC suka kai ziyara ga tsohon Shugaban Kasar.

Ko da yake ba a bayyana makasudin ziyarar ba, an yi amanna cewa ganawar da Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi, wanda kuma shi ne shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, da Muhammadu Badaru Abubakar na Jigawa, da kuma Gwamna David Umahi na Ebonyi – wanda a lokacin bai jima da sauya sheka daga PDP ba – na da alaka da zaben shugaban kasa a 2023.

Daga bisani kuma, a watan Satumban bara wasu shugabannin PDP suka ziyarci Mista Jonathan a Abuja suna rokon shi da kada ya fice daga jam’iyyar.

Wannan ne ya sa wasu ’yan Najeriya cewa idan ba rami, me ya kawo maganar rami? Ma’ana, da babau maganar ficewar Jonathan daga PDP me zai sa shugabannin jam’iyyar daukar wadannan matakai?

Sannan a lokacin zaben gwamnan Jihar Bayelsa a 2019, an ce goyon bayan da Mista Jonathan ya bai wa jam’iyyar APC na cikin dalilan da suka sa dan takararta David Lyon ya yi nasara – ko da yake wani hukuncin Kotun Koli ya yi masa kwalele da kujerar ana saura sa’o’i kadan a rantsar da shi.

A baya-bayan nan kuma, rashin ganin Mista Jonathan a wurin Babban Taron jam’iyyar PDP ya sa an yi ta maganganu.

Idan ta yi wari

Wadannan batutuwa ne dai suka sa wasu hasashen cewa ba batun Mali ba ne kawai ya kai Jonathan Fadar Shugaban Kasa.

Shin akwai wani shiri ne da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi na mayar da mulki ga Goodluck Jonathan a shekarar 2023?

Zuwa yanzu dai daga Buharin har Jonathan babu wanda ya ce uffan a kan lamarin, amma dai ko ma me ake ciki, idan ta yi wari ’yan Najeriya za su ji.