✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakimin da ’yan bindiga suka harba a Zamfara ya rasu

Ya rasu ne sakamakon harbin da maharan suka yi masa

Hakimin ’Yankuzo da ke Karamar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, Kogo Hamza, wanda ’yan bindiga suka harba ya rasu a asibitin da yake samun kulawa.

An harbi basaraken ne a kan hanyar ’Yankuzo zuwa Tsafe, inda aka garzaya da shi Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Gusau, babban birnin jihar, inda ya rasu a daren Asabar.

’Yankuzo dai nan ce mahaifar rikakken dan bindigar nan, Ado Aleiro, wanda sojoji suka ce suna nemansa ruwa a jallo.

Wani dan asalin yankin, Audu Mohammed, ya shaida wa jaridar Punch cewa ’yan bindiga sun kai wa Hakimin harin ne ranar Asabar, lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa fadarsa bayan wani taro da Sarkin Tsafe.

Audu ya ce, “Masu garkuwar sun yi kokarin sace shi ne, amma ya ki tsayawa.

“Hakan ce ta sa suka bi shi suka bude wa motarsa wuta, inda ya sami raunuka daga harbin bindiga.

“An garzaya da shi Babban Asibitin Tsafe, amma daga bisani aka mayar da shi FMC Gusau, inda daga bisani ay rasu a can da daren Asabar.”

Sai dai duk kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Mohammed Shehu kan lamarin ya ci tura saboda wayarsa ta ki shiga har zuwa lokacin hada wannan rahoton.