✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakkin ma’aikata: Babu bukatar yajin aikin NLC —Gwamnati

Gwamnatin jihar ta bakin Hyat ta ce, ta fara kokarin ganin ta warware matsalar albashin ma’aikatan, don haka, ta ce babu bukatar ma’aikatan su shiga…

Gwamnatin Jihar Filato, ta yi kira ga Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) reshen jihar, da ta janye kudirinta na shiga yajin aikin gargadin da ta yi niyyar farawa ranar Litinin.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Shugaban Ma’aikatan Jihar, Mista Sunday Hyat, ya fitar ranar Litinin.

A makon da ya gabata kwamitin sulhu na hadin gwiwa (JNPSNC) reshen Filato, ya ba da sanarwa ma’aikatar jihar za su shiga yajin aikin gargadi na kwana biyar.

JNPSNC ya ce matsalar albashin ma’aikata da sauransu, na daga cikin dalilan da suka sanya yanke shawarar shiga yajin aikin.

Sai dai, gwamnatin jihar ta bakin Hyat ta ce, ta fara kokarin ganin ta warware matsalar albashin ma’aikatan.

Don haka, ta ce babu bukatar ma’aikatan su shiga yajin aiki kafin cimma bukatunsu.

(NAN)