✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin da ambaliya ta jefa manoma a Taraba

Manoma sun tafka asara tare da tsintar kansu a yanayin da ba su taba shiga ba sakamakon ambaliyar ruwa a 2022, shekara 10 bayan irin…

Manoma sun tafka asara tare da tsintar kansu a yanayin da ba su taba shiga ba sakamakon ambaliyar ruwa a 2022, shekara 10 bayan irin hakan a Jihar Taraba.

Mun yi tattaki zuwa yankunan a kwalekwale, inda muka ga yadda ambaliya ta shanye kauyuka da katafarun gonaki gaba daya.

Mun yi kicibus da wani manomi mai shekara 74, wanda ya karbi bashin banki, ya sayar da gidansa ya hada kudin ya yi noman shinkafa, amma ambaliya ta shanye gonarsa ta lalata komai, alhali yana sa ran samun akalla buhu 700.

Ambaliyar ta yi ajalin mutane da dama, ta lalata gidaje da dukiyoyi, tare da mayar da mutane ’yan gudun hijira.

A wannan rahoton, mun ga yadda ambaliya ta gurgunta harkar noma, da halin da manoma suka shiga bayan irin asarar da suka tafka a daidai lokacin da suke sa ran samun dubban buhunan hatsi idan suka yi girbi.