✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin da iyaye suke jefa ’ya’yansu a ciki

A zahirin gaskiya mu matasa muna cikin tsaka-mai wuya kasancewar rayuwa ce ta rana zafi inuwa kuna.

A zahirin gaskiya mu matasa muna cikin tsaka-mai wuya kasancewar rayuwa ce ta rana zafi inuwa kuna.

Mun kasance a bakin wani tafkeken ramin wuta wanda ba kowa ne ke iya ganin wannan wutar ba.

Sai dai babban tashin hankalin shi ne, mu da muke bakin wannan ramin wuta, mu kanmu mun san ba wayonmu ba ne kuma ba dabararmu ko iliminmu ko tarbiyarmu za su ceto mu.

Domin kuwa na cikin wannan rami so suke yi su ja mu ciki, ga shi zuciyarmu tana rudarmu, sannan wadanda muke tare da su ma cewa suke yi kawai gara mu fada!

Idan muka ki to su sai su je su fada. Wasu kuma kawo mana wafta suke yi don su rungume mu mu fada tare!

Kwatsam kuma sai muka ji ana toro mu ta bayanmu, sai a lokacin hakalinmu ya kara tashi.

Domin a lokacin muka gane cewa ashe dukkanmu damu da muke kan gefen ramin da wadanda suke fadawa da wadanda suke ciki, mafiya yawanmu IYAYENMU NE SUKE TURA MU BISA RASHIN SANI.

Abin da nake nufi a nan shi ne iyayenmu na wannan zamani gaba daya sun watsar da kyawawan al’adunmu na Hausawa kuma sun manta da addininmu, gaba daya tarbiyyar da kakanninmu suka yi musu kwata-kwata ba irinta suke yi mana ba.

Suna yin iyakar kokarinsu wajen tura mu makarantar addini da boko da kuma ciyar da mu.

Sai dai suna yin tuya ne suna mantawa da albasa.

Domin kuwa an wayi gari a yau, FASIKANCI, ALFASHA da ZINA sun zama ababen alfahari a tsakanin mu matasa maza da mata.

Matashi zai iya fadi a cikin ’yan uwansa matasa cikin gadara da alfahari cewa na yi ko zan yi ko ina yin zina!

Har an kai matsayin da idan wani ya ce shi bai taba yin alfasha ba, to ya zama abin kallo abin mamaki, abin nunawa, idan ma kai-tsaye ba a karta shi ba kuma duk da cewa da yawansu da iliminsu da kuma tarbiyyarsu.

Misali, akwai wata budurwar wani da na sani ’yar Jihar Kaduna yarinyar ’yar masu kudi ce daidai gwargwado, kawai wata rana sai abu ya ishe ta ta cire kunya ta fuskanci iyayenta ta ce musu ita gaskiya aure take so, amma kawai sai mahaifiyarta ta dalla mata mari a kan cewa wai karatu za ta yi ba aure ba.

To dama kuma babu abin da take boye wa saurayin nan saboda haka ta bayyana masa damuwarta kuma ta neme shi cewa don Allah tana so ya je can garin nasu domin ita ba za ta iya zuwa Kano ba.

Ta ce idan ya je in dai masauki ne ba ya da matsala.

Ni kuma duk abin da yake faruwa a tsakaninsu yana sanar da ni, ko sakon waya ta tura masa sai ya kawo min na gani.

Allah dai Ya kiyaye shi bai je ba saboda na ce ba zan raka shi ba.

Sannan babba ita ce kariyar Ubangijin. Da ta ga yana yi mata wasa da hankali har cewa ta yi za ta turo masa da kudin mota Naira dubu 10, amma bai samu ya je ba.

Bayan wasu ’yan watanni sai take fada masa a waya cewa, “Wane ka ki ka zo, ni kumaa gaskiya na kasa hakuri, na je na samu saurayin kawata mun yi abin da muka yi, har ma na samu juna biyu.

“Ba ka ga yadda hankalin iyayena ya tashi ba.

Sun yi ta kuka suna cewa “WAI ME NA NEMA NA RASA?”

To sai a lokacin wannan maganar ta shiga cikin kaina na ga cewa to me ta nema ta rasa?

Me ta je ta nemo? Me ya sa ba ta je ta nemo abinci ko kayan sawa ba? Abin da ta nema ta rasa ai shi ne ta nemo wannan amsar a zahiri take.

Haka akwai wani wanda bangare guda a gidansu nasa ne shi kadai, babu abin da ya nema ya rasa a cikin kayan jin dadin rayuwa.

Amma haka kullin yake kallon fina-finan batsa. Idan ya gama kallo sai ya tashi ya yi wanka ya yi Sallah raka’a biyu ya tuba ga Ubangiji, amma gobe ma haka zaisake aikatawa.

Yana cikin wannan hali ne wata rana ya ji iyayensa suna hira a tsakaninsu, mamarsa tana ce wa mahaifinsa Abban wane ka san akuyar nan ta gidan gonarmu ta mutu, saboda haka bai kamata a bar bunsurun da ke gonar shi kadai ba.

Sai mahaifin nasa ya ce eh kuma fa gaskiya ne, bari gobe zan sa a je kasuwar kauye a samo masa akuya a hada su.

Kawai sai wannan bawan Allah ya fara tunanin to wai su iyayen nasa sun fi sanin matsalar bunsuru ne a kan matsalar shi dansu ko kuma bunsuru ya fi shi ne a wajensu?

Umar Abubakar Sufi (3rdsufi), Shugaban Shababul Khair Skuad (08163739092, 09080115778)