✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin da makarantun Tsangaya na gwamnati ke ciki a Kano da Jigawa

Har ilimin na’urar Kwamfuta muke koya musu.

A ci gaba da kawo rahoto kan halin da makarantun Tsangaya da gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ta gina a wasu jihohin Arewa da nufin rage yawan almajiran da ke yawon bara a kan tituna, a yau mun leka jihohin Kano da Jigawa ne don ganin halin da suke ciki.

Aminiya ta gano cewa jim kadan bayan saukar tsohon Shugaban Kasar, akasarin makarantun sun fada halin ha’ula’i, inda da yawa daga cikinsu ko dai an rufe su dungurungum, ko kuma suna cikin halin ni-’yasu.

Sai dai a wasu jihohin, akasarin makarantun sun ci gaba da aiki, inda gwamnatocin jihohin suka karbi ragamar gudanar da su, har ma aka kara giggina wasu.

A Jihar Kano, akwai irin wadannan makarantun guda 15 yanzu haka; uku wadanda Goodluck ya gina, 12 kuma Gwamnatin Kano ta kara.

Sai dai masana da dama suna ganin ba za su yi wani muhimmin tasiri ba, kasancewa daliban da suke iya dauka ba su wuce 3,000 ba, musamman in aka yi la’akari da dubban daruruwan almajiran da ake da su a jihar.

Guda ukun da aka gina sun hada da ta garin Kanwa a Karamar Hukumar Madobi da Bunkure a Karamar Hukumar Bunkure sai kuma wata a Bagwai da ke Karamar Hukumar Bagwai.

Daga bisani, Gwamnatin Jihar Kano ta sake gina wasu 12 a sassan jihar, wadanda suka hada da Dandinshe a Karamar Hukumar Dala, Kanwa I da Kanwa II (a Madobi) da Warawa (a Warawa) da Tsakuwa a Dawakin Kudu (ta ’yan mata) da Kibiya (a Kibiya) da Ganduje (a Dawakin Tofa) da Garo da Kabo (Kabo) da Albasu (a Albasu) da Bichi da Gaya (na je-ka-kadawo).

Ko a watannin baya, Gwamnatin Jihar ta debi sababbin alarammomi 60, ta tura wa kowace daga cikin tsangayun 15 malamai hudu kuma sun fara aiki.

‘Akasarin tsangayun na aiki a Kano’

Aminiya ta gano cewa dukkan makarantun 12 suna aiki, koda yake suna fama da kalubalen gudanarwa nan da can.

A ziyarar da wakilinmu ya kai daya daga cikin makarantun da ke Dandinshe, ya iske dalibai suna tsakiyar karatun Alkur’ani da yamma.

A cewar Mataimakin Hedmastan Makarantar, Malam Muhammad Rabi’u Isma’il, makarantar tana da dalibai sama da 80, kuma ana koya musu darussan boko da safe, da yamma kuma a yi musu na Islamiyya da Alkur’ani.

‘Dalibai sukan sauke Alkur’ani kafin su kammala karatu’

Malam Muhammad ya ce, “Muna da matakin ajujuwa hudu, kuma duk wanda ya kammala makarantar, kamar ya kammala firamare ce, don akwai wadanda sun gama mun ba su shaida sun dora a wasu makarantun sakandare.

“Tsarin da muke tafiya a kansa a nan shi ne duk wanda ya kammala karatu a nan, akalla yana sauke Alkur’ani, wadansu ma mu kan yi sa’a su haddace wani bangare, wadansu kuma ma su haddace gaba daya.

“Bangaren abinci kuma, gwamnati ce take ba su abinci sau uku kullum, kuma iri daban-daban.

“Muna da malamai wadanda gwamnati ta dauka, akwai kuma wadanda PTA ta kawo,” inji shi.

Da Aminiya ta tambaye shi ko akwai daliban da suka fito daga wasu jihohin, ya ce dukkansu ’yan asalin Jihar Kano ne.

Akwai ruwa da wuta, amma babu asibiti

Aminiya ta gano akwai rijiyar burtsatse da take samar wa makarantar ruwa a koyaushe, da kuma wutar lantarki. Amma ta lura akasarin makarantun babu dakin shan magani ko wajen duba daliban in ba su da lafiya.

Shi kuwa wani dalibi a tsangayar, Isah Musa, ya ce ana koya musu darussan Hausa da Ingilishi da Lissafi da Kwamfuta a bangaren boko.

“A bangaren Islamiyya kuma, ana koya mana Tajwidi da Alkur’ani da Larabci, kuma ana ba mu abinci sau uku kullum. Yanzu haka zan iya karatu da harufan boko,” inji shi.

A ragowar makarantun da Aminiya ta ziyarta a Warawa da Bunkure, kusan duk yanayin iri daya ne, koda yake akwai wadanda an riga an dibi sababbin dalibai, amma ba su fara karatu ba.

A bangaren makwanci kuwa, akwai dakunan kwanan dalibai da suke da fankoki, amma mun lura babu gadaje, daliban a tabarmi suke kwana.

Bugu da kari, a akasarin makarantun da wakilin namu ya ziyarta, galibin ajujuwan ko dai ba su da wadatattun kujeru, ko kuma sun karairaye.

Amma a Bunkure da Kanwa da Bagwai kuwa, kusan dukkan makarantun an sabunta gin-ginensu, an zuba sababbin kujeru a ajujuwa da gadaje a dakunan kwanan dalibai, har ma da na’urorin Kwamfuta da dakunan gwaje-gwajen kimiyya.

‘Dalibai ba sa biyan ko sisi’

A tattaunawarsa da Aminiya, Shugaban Hukumar Kula da Makarantun Islamiyyah da Tsangayu ta Jihar Kano, Gwani Yahuza Gwani Danzarga, ya ce dukkan daliban ba sa biyan ko kwabo, gwamnati ta dauki nauyinsu kuma tana ciyar da su sau uku a kullum.

Ya ce, “Saboda yadda mutane suka karbi abin hannu bibbiyu yanzu haka, mukan tattara sunan dukkan masu son sa ’ya’yansu a ciki, sannan mun tantance wadanda suka cancanta mu ba su gurbin karatu a ciki daga ofishin hukumarmu.

“Yanzu haka, muna da dalibai kusan 3,000, kuma muna da shirye-shirye dabandaban wajen sake inganta su ta hanyar gina sababbin ajujuwa da dibar sababbin malamai.

“Kazalika, akwai wasu kungiyoyi masu zaman kansu kamar su KDF da ADF da sauran masu hannu da shuni da ma UNICEF duk suna tallafa wa wadannan makarantu.

“An debi sababbin dalibai a Bunkure da Kanwa, kuma ana ci gaba da gyare-gyare, sai dai dalibai ba su koma sun fara karatu ba.

“Amma ita ta Bagwai, akwai dalibai a ciki, akwai na Ganduje da aka mayar da su can saboda ana gyare-gyare a tasu, sai kuma ta Doguwa lokacin da rashin tsaro ya yi yawa aka mayar da su Bagwai, amma muna shirin mayar da su can.”

Dole jihohi su yi irin wannan tsari kafin a kawo karshen bara — Gwani Danzarga

Sai dai ya yi kira ga daidaikun mutane da kungiyoyi su taimaka wa wadannan makarantu, tare da kiran sauran jihohin Arewa su kwaikwayi irin wannan tsari, matukar ana so a kawo karshen gararambar almajirai a kan tituna.

Dangane da tsangayun da ba na gwamnati ba kuwa, Gwani Yahuza ya ce, “Yanzu haka tsangayun da ba na gwamnati ba, muna da wani shirin da muke son tabbatar da duk alaramman da zai dauki dalibai an kawo masa su tare da abincinsu, kuma kowane dalibi ya kai akalla shekara 15.

Akwai tsangayun gwamnati guda bakwai da ke aiki a Jigawa Kamar a takwararta Kano, Jihar Jigawa na da makarantun Tsangaya guda bakwai, wadanda tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya gina a kananan hukumomin jihar.

Wadannan tsangayu sun hada da ta Gantsa (a Buji) da ta Zango (a Taura) da ta Mai’aduwa (a Gagarawa) da ta Gwiwa da ta Sule-Tankarkar da ta Birniwa da kuma ta Kirikasamma.

Rahotanni sun nuna baya ga kasancewar dukkan makarantun yanzu suna aiki a karkashin Hukumar Ilimin Bai-Daya ta Jihar (SUBEB), gwamnati ta kuma kara yi wa wasu alarammomin karin gine-gine har guda 39.

Sai dai kai-tsaye ba ita take gudanar da su ba, amma ta taimaka wajen yi musu gini na zamani, ciki har da ajujuwan karatu da dakunan kwanan dalibai, yayin da akan surka wa dalibai da wasu darussan boko da na Alkur’ani ko Islamiyya.

A ziyarar da wakilinmu ya kai irin wannan Tsangaya, wato tsangayar Gwani Suhailu da ke garin Kargo a Karamar Hukumar Dutse, ya iske almajirai sanye da kayan makaranta suna karatu a cikin ajujuwansu, kuma sun ce akan koya musu darussan boko a ciki.

Gwani Suhailu dai ya ce Tsangayar, wacce dama can tana da dalibai kafin a taimaka musu da ginin, ya ce yanzu haka akwai dalibai sama da 150, ciki har da maza da mata.

‘Har ilimin na’urar Kwamfuta muke koya musu’

A Tsangayar garin Gantsa kuwa, Hedimastan Makarantar, Malam Ado Abdulkadir, ya ce makarantar tana da dalibai 204, kuma dukkansu ’yan asalin jihar ne.

Ya ce, “Baya ga ilimin Alkur’ani da na Islamiyya, muna koya musu darussan Ingilishi da Lissafi da Ilimin Zamantakewa da Na’urar Kwamfuta da Kimiyya da Hausa da Larabci da sauransu.

“Muna da malamai akalla guda tara, kuma muna da likita da dakin shan magani sannan sau uku ake ciyar da dalibai, dukkansu ba sa biyan kudi.

“Kalubalen da kawai muke da shi bai wuce na wutar lantarki ba, wanda a sakamakon haka, ba koyaushe muke iya koya musu na’urar Kwamfuta ba, muna kira ga gwamnati da sauran masu hannu da shuni su shigo don tallafawa ta wannan bangare,” inji Hedimastan.

Wakilinmu ya gane wa idonsa dakin na’urorin Kwamfuta da dakin shan maganin da kuma ajujuwan makarantar da dakunan kwanan dalibai da gidajen malamai, kuma galibinsu suna cikin yanayi mai kyau.

‘Akwai dalibai sama da 700 a tsangayun gwamnati’

Usman Muhammad Shettima, Daraktan Sashen a Makarantun Tsangaya, ya ce tsangayun gwamnati na da jimillar dalibai sama da 700, ban da wadanda gwamnati ta gina wa alarammomi 39, wadanda ba a karkashinta suke kai-tsaye ba.

Ya ce, “Kwanan nan ma adadin zai karu saboda muna gab da dibar sababbin dalibai. Mun tanadar musu abinci sau uku a kullum, da kayan makaranta da kuma kayan koyo da koyarwa.

“Bugu da kari, ganin irin hobbasan da gwamnati ta yi, wata kungiyar kasa da kasa mai tallafa wa ilimi a matakin farko, wato BESDA, ta rungumi tsangayu akalla 480 a kananan hukumomi 17 na jihar nan.

“Suna daukar nauyin malaman da daliban, har ma suna ciyar da su abinci.

“Ina da kwarin gwiwar matukar muka ci gaba da wannan kokari na taimakekeniya, wata rana za a wayi gari almajirai sun daina yawon bara baki daya,” inji Darakta Shettima.

Masana dai da sauran masu ruwa-datsaki na ganin matukar ana so almajirai su daina yawon bara, to tilas sai dukkan jihohin Arewa sun samar da ingantattun tsare-tsare na bai-daya a harkar.

Kazalika, sun ba da shawarar cewa dole ne kungiyoyi masu zaman kansu da masu hannu da shuni su shiga a dama da su ta hanyar kawo nasu daukin.