✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin da maniyyata ke ciki bayan alhazai sun dau harama

Matsayin maniyyatan da ba su samu sauke farali ba bayan alhazai sun dau harama.

A yayin da alhazan wannan shekara suke isa Mina a ci gaba a ayyukan ibada na sauke faran aikin Hajjin bana, maniyyata sun bayyana takaicinsu bisa matakin da kasar Saudiyya ta dauka na takaita aikin Hajjin bana ga iya mazauna kasar.

A ranar Litinin alhazan wannan shekara su kimanin 60,000 za su yi hawan Arfa; A halin yanzu suna riga suka yi Umrah a Haramin Makkah, inda daga bisani za su wuce zuwa Mina kafin su garzaya zuwa filin Arfa —Tara ga watan Zhul-Hijjah.

Tun daga lokacin da hukumomin Saudiyya suka sanar da daukar matakin sake takaita aikin Hajji zuwa mazauna kasar saboda cutar COVID-19 ake ta maganganu game da matakin.

Yawancin maniyyata da suka biya kudinsu a Jihar aknao sun bayyana rashin jin dadinsu da cewa kai tsaye matakin na Saudiyya ya hana su cika burinsu na son sauke farali.

Takaicin maniyyata

Wani maniyyaci wanda bai taba zuwa aikin Hajji ba, Malam Umar Sani, ya bayyana takaicinsa game da hana mazauna kasashen waje aikin Hajji a bana.

Ya ce, “Ai a yi batun rashin jin dadi ma bai taso ba. Dole ne wanda ya yi niyyar yin wannan ibada, in ya samu wannan labarin ransa ya baci. Amma kasancewar mutum babu abin da zai iya yi dole ya hakura.”

Ita ma wata maniyyaciya, Malama Rukayya Abubakar, ta ce lamarin ya sanya ta cikin damuwa saboda shekara biyu ke nan take biyan kudinta na Hajji amma ba ta samun damar tafiya.

“A gaskiya ban ji dadin lamarin ba, domin bara mun biya aka yi batun cutar COVID-19 wanda a lokacin mun san akwi cutar.

“Bana muna ta murna har mun fara shirye-shiryen tafiya domin har an yi mana bita; Sai kawai muka ji wanan bakin labarin.”

Mayar da kudin maniyyata

Bayan sanarwar ta Saudiyya ce Hukumar Jin dadin Alahazai ta Jihar Kano ta kafa kwamiti don fara shirye-shiryen mayar wa maniyyatan kudadensu, kamar yadda shugaban Hukumar, Abba Dambatta ya shaida wa ’yan jarida.

Ya ce za a mayar wa maniyyatan kudinsu ne ta banki da zarar kwamitin ya kammala aikin nasa.

Dambatta ya kara da cewa kwamitin ya kunshi masu ruwa da tsaki daga jami’an Hukumar da kuma jami’an tsaro da kuma wakilai daga Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Hana Cin Hanzi da Rashawa ta Jihar Kano don gudanar da aikin cikin nasara.

Karbar kudi ko jiran badi

Malama Rukayya Abubakar, ta biya kudin Hajji ta hannun Hukumar, amma ta ce ta dauki lamarin a matsayin kaddara, don haka za ta ci gaba da barin kudinta a hannunan Hukumar zuwa badi.

“A gaskiya ba zan karbi kudin nan ba domin idan na karba ma babu abin da zan iya yi da su; Za mu ci gaba da jira zuwa badi mu ga abin da Allah zai yi,” inji ta.

Malam Umar kuma ya ce, “Ni dai kudina zan karba na juya na sa su a wani kasuwancin, ban san abin da zan samu kafin shekarar ba.

“Muna dai fatan badi mu samu mu gudanar da wanann ibada insha Allah.”

Amma wata maniyyaciya mai suna Malama Rabi Ali, ta ce duk da cewa abu ne na rashin jin dadi, amma ta mayar da lamarin ga Allah.

“To dan Adam duk abin da yake yi akwai kaddara. Da ma tun farko Allah Bai yi za mu yi wanann ibada a bana ba.”

Game da batun kudi kuma, Malama Rabi ta ce za ta karba ba domin tana da burin zuwa a badi domin ta samu shiga a sahun farko.

“Kin san yawanci idan za a fara shirye-shiryen tafiyar badi to da mutanen da suka bar kudinsu za a fara.

“Don haka ba zan karbi kudina ba, zan bar su a hannun Hukumar Alhazai har sai Allah Ya kai mu badin mu sake gwadawa.”

Za a yarda da matakin Saudiyya ba?

Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khaleel, ya shaida wa Aminiya cewa ba dole ne a yarda da dalilan da Saudiyya ta bayar na daukar matakin hana baki zuwa aikin Hajjin ba.

Amma ya bayyana cewa wajibi ne a yi wa dokar biyayya.

Sheik Ibrahim Khaleel ya ce, “Duk da cewa ana ci gaba da taruka a duniya na su kwallon kafa da sauransu amma Saudiyyar ta dauki wanann mataki, to wajibi ne a yi wa dokokinta biyayya.

“Kasancewar a kasarta ake gudanar da Aikin Hajjin, ita ce mai ruwa da tsaki a harkar aikin Hajji.

“Abin da ake duba shi ne biyayya da kuma hadin kai don kada a samu baraka. Wannan shi ne tsari na Addinin Musulunci.”

Maniyyatan da COVID-19 ta hana sauke farali

Game da hukuncin maniyyatan da hakan ta faru da su malamin ya bayayan cewa “Dukkaninsu suna da ladan Aikin Hajji matukar ba su yi zage-zage a kan lamarin ba.

Wannan radadin da suke ji na hana sun da aka yi Allah zai ba su lada. Ga ladan aikin Hajji ga kuma ladan hakuri.”

Malamin ya kuma yi kira gare su da su rungumi kaddara, “Su yi hakuri, wani lokaci zai so nan gaba da za su yi. Abin zai wuce.”

Shi ma Limamin Masallacin Juma’a na Masallacin Juma’a na Triumph, Malam Lawan Abubakar, ya bayyana cewa ko ma wane dalili ne ya sanya kasar Saudiyya ta hana baki zuwa aikin Hajji to babu abin da Musulmi zai yi sai hakuri.

Ya bayyana cewa maniyyata za su sami ladan aikin Hajji.

Sunnar Manzon Allah ce

“Manzon Allah SAW ya bayyana cewa wanda ya yi niyyar aikin Hajji, ya tafi hanya aka tare shi, aka hana shi shiga kasar, to ya yanka abin yankansa ya kuma yi aski; Zai zama yana da lada kamar wanda ya yi aikin Hajji.

“Hakan ta faru ga Manzon Allah (SAW). Ya daura niyyar aikin Hajji har ya kusa shigowa Makka sai kafirai suka hana shi shiga; Don haka ya tsaya a wanann wuri ya yanka abin yankansa ya kuma yi aski.”

Har ila yau Malamin ya yi kira ga maniyyatan da hakan ta faru gare su da su yi hakuri kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya yi a wancan lokaci.

“Babu abin da mutum zai yi sai ya yi hakuri domin shi ne abin da Manzon Allah (SAW) ya yi a wancan lokaci da kafirai suka hana shi gudanar da aikin Hajji.

Malamin ya bayyana cewa, “Da Allah Ya ce ya yi hakuri a kan abin da aka yi masa, ba wai Allah yana goyon bayan abin da kafiran suka yi ba [ne], sai dai yana yi ne don a hakurkurtar da Manzon Allah (SAW) a kan abin da ya same shi na rashin jin dadi.”

Yadda masu zirga-zirgar aikin Hajji suka ji

Alhaji Abdurrazak Ibrahim shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Harkar zirga-zirgar Aikin Hajji da Umara, shiyyar Arewacin Najeriya, kuma Shugaban Kamfanin zirga-zirga na Muslima Travel Agency.

Ya bayyana rashin jin dadinsu kan matakin na Saudiyya duba da cewa hakan kai tsaye ya taba kasuwancin ’ya’yan kungiyar.

“Duk da cewa ba mu ji dadin abin ba amma babu yadda za mu yi sai hakuri.

“Saboda harkokin cin abincinmu sun tabu. Sai dai mu yi fatan Allah Ya kai mu badi, kuma mu yi fatan kada wani abu ya sake zuwa ya zame mana matsala.

“Domin idan an duba da farko ai Saudiyyan ta amince da za a yi aikin Hajjin, daga baya ta ce dole sai duk maniyayta sun karbi alluransu zagaye na farko da na biyun da aka tsara; Sai ya kasance wasu kasashen ma yanzu suke karbar allurar ta farko.

“Kuma sun yi lissafi wasu ba za a gama karba ba har lokacin aikin Hajji ya yi, don haka suka dauki wanann mataki.

“To ko ma dai mene ne, muna addu’ar Allah Ya kawo mana karshen wanann matsala,” inji shi.

Wannan dai shi ne karo na biyua jere da maniyyatan suke kudurta zuwa aikin Hajji amma hakan bai yiwu ba.

A shekarar 2020 Saudiyya ta taikata gudanar da Aikin Hajjin ga maniyyata 10,000 da ke cikin kasar sakamakon barkewar cutar COVID-19.