✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hamas ta kashe sojojin Isra’ila bayan harba rokoki 1,500

Rikici tsakanin Falasdinawa da Isra'ila ya kara makari a yankin Zirin Gaza.

Kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta tabbatar da hallaka sojojin Israe’la bayan sun yi wa Isra’ila ruwan rokoki.

Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF) ta cewa kungiyoyin Falasdinawa sun harbo akalla makaman roka guda 1,500 a cikin kwanan ukun da suka gabata.

Hamas ta ce a za ta ci gaba da yi Isra’ila ruwan wuta, a yayin da Isra’ila ta kashe wasu kwamandojinta ta harin sama a yankin Zirin Gaza.

Tun makon jiya rikici ke kara tsanani tsakanin bangarorin, tare da sanadiyyar kai wa Isra’ila hare-haren na ramuwar gayya bayan ta kai wa kungiyoyi da wasu yankunin Falasindawa hare-hare.

Kasashen biyu sun yi ta harba rokoki a tsakanin su, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa 56 da kuma Yahudawa shida.

Falasdinawa 200 da Yahudawa 100 ne aka jikkata a musayar wutar, a yayin da kungiyar Hamas ta tabbar cewa hare-haren Isra’ila a yankin Zirin Gaza ya yi ajalin wasu kwamandojinta 15.

A ranar Larabar, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi zmaa na musamman kan rikicin, amma ya kasa cimma matsaya kan sanarwar da zai fitar.