Hambararren Shugaban Guinea, Alpha Conde, ya tafi Dubai neman lafiya | Aminiya

Hambararren Shugaban Guinea, Alpha Conde, ya tafi Dubai neman lafiya

Guinea’s President Alpha Conde attends a news conference following a meeting with French President Emmanuel Macron at the Elysee Palace in Paris, November 22, 2017. REUTERS/Philippe Wojazer – RC1DB5DC7C10
Guinea’s President Alpha Conde attends a news conference following a meeting with French President Emmanuel Macron at the Elysee Palace in Paris, November 22, 2017. REUTERS/Philippe Wojazer – RC1DB5DC7C10
    Abubakar Muhammad Usman

Bayan shafe tsawon wata hudu a hannun dakarun sojoji, hambararren Shugaban Kasar Guinea, Alpha Conde, ya tafi Daular Larabawa, don duba lafiyarsa.

Tsohon Shugaban mai shekara 83, ya fara fama da rashin lafiya ne tun bayan da sojoji karkashin jagorancin Mahamat Dambouya suka hambarar da gwamnatinsa kuma suke tsare da shi.

Fama da rashin lafiyar ne ya tilasta masa bukatar barin kasar zuwa Dubai, don duba lafiyarsa, duk da cewa babu cikakken bayani game da ciwon da ke damunsa.

Sojojin kasar dai sun hambarar da gwamnatin Conde a watan Satumbar 2021, bayan da ya sake lashe zaben kasar karo na uku, duk da mummunar zanga-zangar adawa da aka yi masa.

Conde dai ya samu damar sake zama shugaban kasar a karo na uku ne bayan da ya yi wa Kundin Tsarin Mulkin kasar kwaskwarima, abin da ya ba shi damar sake tsayawa takara tare da lashe zaben.

Da farko sojojin da suka hambarar da gwamnatin ta shi, sun sha alwashin hana shi fita daga kasar sakamakon yunkurinsu na gurfanar da shi gaban kotu kan zargin aikata laifuka a lokacin mulkinsa.

Sai dai tsamarin da jikin nasa ya yi, ya sanya suka yanke shawarar barinsa tafiya Dubai don duba lafiyarsa.