✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Hana jiragen wasu kasashe shiga Najeriya ya yi daidai’

Shugaban kamfanin jiragen Air peace, Mista Allen Onyema, ya yaba wa matakin da Gwamnatin Najeriya ta dauka na hana shigowar jiragen sama daga wasu kasashe.…

Shugaban kamfanin jiragen Air peace, Mista Allen Onyema, ya yaba wa matakin da Gwamnatin Najeriya ta dauka na hana shigowar jiragen sama daga wasu kasashe.

Matakin ya biyo bayan yunkurin gwamnati na bude hada-hadar jiragen sama zuwa kasashen waje.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya bayyana a ranar Alhamis cewar, jiragen kasashen da suka yarda ‘yan Najeriya su shiga kasarsu kadai za a ba damar shigowa Najeriya.

Sirika ya kuma ce an dauki matakin ne domin a kare martabar ‘yan Najeriya a kasashen da aka hana su shiga.

Onyema ya ce hakan zai kara daga darajar ‘yan Najeriya a idon duniya da kuma nuna wa jiragen kasashen wajen cewar Najeriya ba za ta kara daukar raini ba.

A wasikar da Onyema ya aika wa Ministan ya ce, matakin ya kawo sabon sauyin ci gaba da hukumar sufurin jiragen ta samu.

“Lallai natakin da ka dauka zai kawo wa ‘yan kasa da kasar nan mutunci. ‘Yan Najeriya a fadin duniya za su rika tafiya a mutunce tun daga ranar da wannan labarin ya kai musu.

“Wannan wani sabon babi ne na kawo karshen tsangwama da ake yi wa ‘yan Najeriya da duk wani abu da ya fito daga kasar nan”, inji Onyema.

Ya kuma yaba wa Sirika kan sauye-sauyen da ya kawo a harkar sufurin jiragen sama, da kuma kokarin ganin jiragen Najeriya kawai suka yi jigilar ‘yan Najeriya da gwamnatin tarayya ta kwaso daga kasashen waje.