✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hana mu Dala ta jefa Naira a mawuyacin hali — ’Yan canji

Mutum na farko da ya janyo tashin farashin Dala shi ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya.

Kimanin wata biyu ke nan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya hana sayar da Dalar Amurka ga ’yan canji masu lasisi da ake kira ’yan BDC, wanda hakan ya jefa kasuwar canjin a mawuyacin hali.

Aminiya ta ziyarci wasu daga cikin kasuwanin ‘yan canjin a Legas domin ganin halin da suke ciki, inda ta iske kasuwannin ’yan canjin sun koma kamar kufai babu hada-hadar da aka saba gani a baya.

Haka nan mafi yawan ofisoshin ’yan canjin suna rufe yayin da daidaikun mutane da suka fito kasuwar suke zazzaune a gefen rumfunansu wadansu a kwankwance a masallaci yayin da wadansusu ke yin nafilfili.

Alhaji Musa Shu’aibu Dansudu, daya daga cikin shugabanin ’yan canjin Kasuwar Irik a Legas, ya yi zargin cewa, mutum na farko da ya janyo hauhawar farashin Dala shi ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Godwin Emefeile.

Ya ce sai kuma mutanen da aka bai wa dama suka yi kutse a kasuwar canjin wadanda ba ’yan canji ba ne.

Alhaji Musa Dansudu, ya ce abin da ya janyo tsadar Dalar shi ne ba kaitsaye Bankin CBN, yake bai wa masu BDC Dala ba, sai ya bai wa wani kamfani sannan kamfanin ya dora tasa ribar kafin ya bai wa masu BDC, bayan masu BDC sun yi rajista ne kaitsaye da Bankin CBN.

“Bayan wannan kuma akwai tsarin da Gwamnan CBN ya kawo, inda ya ba da umarnin duk masu BDC sai sun ajiye Naira miliyan 35 wadanda za su yi wata biyar zuwa shida a ajiye.

Wannan tsarin ya sa da yawa daga cikin ainihin ’yan canjin an fitar da su daga harkar saboda ba su da kudi su kuma barayin gwamnati da ’yan siyasa sai suka samu dama suka shiga harkar gadan-gadan suna karbar Dala su kai kasashen waje su sayar, su kai Hong Kong da Dubai.

Wannan shi ne ainihin musababbin lalacewar darajar Naira da tashin goron zabo da take yi, idan ana so a samu sauki sai an koma baya an yi amfani da tsarin Bankin CBN na lokacin mulki Obasanjo zuwa Goodluck, sanan a koma a bibiyi yadda ake bai wa ’yan canji Dala a lokacin mulkin Janar Sani Abacha,” inji shi.

Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu ya ce muddinBankin CBN bai sauya salo, ya yi gyare-gyare ba, Dalar Amurka za ta ci gaba da tsada da karanci yayin da darajar Naira za ta ci gaba da faduwa.

Alhaji Musa Shu’aibu Dansudu daya daga cikin masu hada-hada a kasuwar ’yan canji da ke Legas, ya shaida wa Aminiya cewa zuwa yanzu dukkansu suna cikin matsi kasancewar Dalar ba ta samuwa.

“A baya a duk mako Bankin CBN yana ba mu Dala dubu 20, dubu goma-goma sau biyu a mako, amma a yanzu ba a samu domin an dakatar.

“Idan ka yi lissafi koda a ce mutum biyar ne suke aiki a kowane Kamfanin BDC wanda ake da samar da Naira dubu 5500 za ka ga mutanen da suka rasa aiki a sanadiyar wannan mataki suna da yawa sosai, baya ga wadanda suke dogaro da su.

To ka ga wannan mataki ba karamar illa zai yi ba, kuma in ka lura kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, domin har yanzu farashin Dalar bai sauka ba sai ma kara hauhawa da ya yi.

Kafin a daina ba da Dalar ga BDC ana sayenta ce a kan naira dari hudu da doriya, amma yanzu ta haura Naira dari biyar saboda karancin data yi.

“Don haka, a ganina kamata ya yi gwamnati ta duba wannan lamari ta duba yiwuwar dawo da bai wa ’yan canji Dala, in ya so sai a dauki matakai a sanya ka’idoji.

“Domin ko a baya ma abin da ake bayarwa bai wadata ba, don haka farashin yake hauhawa, duk abin da ya yi karanci farashinsa zai hau, amma idan ya wadatu za a samu saukin farashin,” inji shi.

Alhaji Shu’aibu ya ce kamata ya yi a rubanya yawan Dalar da ake ba BDC, sai a sa ido a tabbatar suna sayar wa wadanda suka dace a kan farashin da ya dace, duk wanda kuma ya saba wa ka’ida sai a hukunta shi.

“Wannan ne hanyar da za a bi a samu mafita” inji Musa Shu’aibu.

A bangaren Mukhtar Jama’are wanda shi ma yake gudanar da harkoki a kasuwar ’yan canji a Legas cewa ya yi matakin da CBN ya dauka na daina bai wa masu BDC Dala ya jefa dubban mutane cikin garari.

Ya ce lamarin ba ’yan canji kadai ya shafa ba, ya shafi mutane da dama da suke dogaro da ’yan kasuwar canjin, don haka ya yi kira da gwamnatin Shugaba Buhari ta sake duba lamarin ta kawo masu dauki.

Mukhtar Jama’are ya ce idan akwai bara-gurbi a cikin masu BDC kamata ya yi bincike ya nuna haka sannan a hukunta wadanda binciken ya tabbatar masu laifi ne, amma yi wa harkar kudin goro ba zai haifar da da mai ido ba.