✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hana sana’ar Acaba da hakar ma’adinai ba alheri ba ne —Action Aid

Action Aid ta yi wa Ministan Shari'a raddi.

Kungiyar Bayar da Agaji ta Kasa da Kasa, Action Aid, ta bayyana cewa hana sana’ar Acaba da kuma hakar ma’adinai da ake shirin yi, ba alheri ba ne ga kasar.

Action Aid ta yi gargadin cewa, ba abin da hakan zai janyo wa kasa illa karin fatara da matsalar tsaro.

Wannan gargadi na zuwa ne a matsayin martani ga wata sanarwa da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi na cewa, gwamnatin tarayya na tunanin haramta sana’ar Acaba da kuma hakar ma’adinai da ake yi, a kokarinta na dakile ayyukan ta’addanci.

Kungiyar ta ce, hana sana’ar Acaba da kuma hakar ma’adinai da gwamnatin tarayya ke shirin yi ka iya toshe hanyoyin samun kudin sayen makami, da kuma samun abubuwan masarufi na ‘yan ta’adda, amma ba ta yi tunanin tasirin hakan ga talakawa ba.

A cewar Action Aid, “Kamata ya yi wannan shiri na hana sana’ar Acaba da kuma hakar ma’adinai a tafi da shi tare da wani tsarin da hanawar ba za ta jefa sauran talakawa cikin halin ni ‘ya su ba, la’akari da tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan.

“Domin wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa, yawan matalauta a Najeria zai karu zuwa miliyan 95.1 a shekarar 2022.

Action Aid ta ce yawan wadanda suke fada wa talauci a Najeriya ya karu ne a sakamakon annobar cutar COVID–19, da yawan jama’a, da hauhawar farashi, da kuma tasirin mamayar da Rasha ke yi a Ukraine.

Don haka zai yi wahala gwamnatin tarayya ta shawo kan karuwar aikata mayan laifuka, da shawo kan fatara idan ba wani tanadi ta yi na rage radadin abin da ka iya faruwa ba idan ta yi wannan hani.