✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hango jiragen soji ya sa ’yan ISWAP guduwa su bar mutanen da suka sace a Borno

A ranar Asabar ce mayakan ISWAP suka sace mutanen a Gubio

’Yan ta’addan ISWAP da suka sace jami’an tsaron nan su bakwai, ciki har da dan sanda daya a jihar Borno sun ranta a na kare bayan hango jirgin yakin sojojin sama samfurin Super Tucano yana farautarsu.

Da sanyin safiyar Asabar ce dai ’yan ta’addan suka sace dan sanda daya da kuma jami’an tsaron rundunar tsaro ta CJTF da mafarauta su bakwai a karamar hukumar Gubio ta Arewa maso Gabashin jihar Borno.

Wata majiyar ’yan sanda a baya ta shaida wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tayar da kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Tafkin Chadi, yadda aka kai wa jami’an tsaro hari tare da yiN awon gaba da mutanen a wata RUGA da ke kauyen Pompom Baliya mai tazarar kilomita biyar daga Gubio.

Majiyar ta ce dakarun rundunar Operation Hadin Kai, Gubio da ke samun goyon bayan Rundunar Sojojin Sama da ke dauke da  Super Tucano, sun fatattaki ‘yan ta’addan har ya kai su ga gudu suka nufi hanyar kauyen Gadai da ke karamar hukumar Nganzai.

Wani jami’in leken asiri ya shaida wa Zagazolan cewa ’yan ta’addan sun tsare wadanda abin ya shafa amma da ganin isowar Super Tucano sai suka yi watsi da su nan take suka tsere zuwa cikin daji don tsira da ransu.

“A lokacin ne wadanda lamarin ya ritsa da su, su ma suka gudu zuwa wata hanya ta daban suka tsere daga hannun ’yan ta’addan,” inji shi.

Ya ce jami’an tsaro guda shida, suna cikin koshin lafiya kuma wasu sun dawo garin Gubio yayin da daya ke kan hanyarsa ta dawowa.

“Wadanda aka sa ce daga bisani suka tsira sun hada da dan sanda daya, rundunar hadin gwiwa ta farar hula uku da mafarauta biyu,” inji shi.