✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanifa: Ba a cikin hayyacina na yi batutuwan da na yi a baya ba —Abdulmalik Tanko

Duk bayanan da na bayar a baya ba na cikin hayyacina.

Abdulmalik Tanko, mutumin nan wanda ake tuhuma da kisan dalibarsa ya zargi jami’an tsaro da tilasta shi wajen bayyana batun yadda lamarin kisan Hanifa ya gudana.

Abdulmalik Tanko ya yi wannan zargi ne yayin da yake wa kotu bayani game da shaidu guda shidan da masu shigar da kara suka gabatar yayin zaman kotun da ya gudana a ranakun Laraba da Alhamis.

Abdulmalik ya bayyana wa kotu cewa dukkanin bayanan da ya bayar a baya ba ya cikin hayyacinsa sakamakon barazana ta duka da cin zarafi da jami’an tsaro suka yi masa a kan cewa lallai sai ya bayyana abin da ya faru.

Ita ma wacce ake zargi ta uku, Fatima Jibril Musa ta ce bayanan da ta bayar ta yi su ne bisa tsoron abin da zai biyo baya daga jami’an tsaro duba da cin zarafi da azabar da ta ga jami’an tsaron sun yi wa Abdulmalik Tankon.

Da yake yin karin haske game da dalilin da ya sa wadanda ake zargi suka yi wa kotun bayanan cin zarafinsu da jami’an tsaro suka yi, lauyansu Barista Usman Labaran Kabo, ya bayyana cewa suna so kotu ta yi hukunci akan halacci ko akasin haka akan karbar bayanan wadanda ake zargin wanda kuma suka yi shi ba a cikin hayyacinsu ba.

Tunda farko a zaman kotun na ranar Alhamis masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Musa Abdullahi Lawan sun gabatar wa kotu ragowar shaidunsu guda hudu da suka hada da wata mata mai suna Jummai Danladi wacce Abdulmalik ya yi amfani da wayarta wajen kiran mahaifiyar Hanifa Abubakar, inda ta gaya wa kotu cewa wayar ta bata ne a Keke Napep inda shi kuma Abdulmalik ya yi amfani da ita.

Haka kuma, masu gabatar da kara sun gabatar da matar Abdulmalik Tanko mai suna Jamila Muhammad Sani a matsayin shaidarsu wacce ta bayyana wa kotun yadda mijinta ya kawo yarinya Hanifa ya ce ’yar abokiyar aikinsa ce za ta zauna a wurinsu na ’yan kwanaki kafin mahaifiyarta ta dawo daga Abuja.

Jamila ta shaida wa kotu cewa da farko Hanifa ta so bijirewa zaman gidan sakamakon kuka da ta fara kafin daga bisani ta saba da yaran gidan guda biyu.

Jamila ta ci gaba da shaida wa kotu cewa, cikin dare misalin karfe 11 na dare bayan ta shafe kusan kwanaki biyar mijin nata ya tashi Hanifa daga barci da nufin zai kaita wajen mahaifiyarta.

“Ranar Alhamis Hanifa tana barci misalin karfe 11 na dare ya tashe ta ya karbi kayan makarantarta da nufin zai mayar da ita wajen mahaifiyarta.

“Na nemi ya bar ta sai washegari amma ya tafi. Ban san lokacin da ya dawo gida ba domin na yi barci.”

Ta shaida wa kotu cewa ba ta sami labarin bacewar Hanifa ba har sai lokacin da jami’an tsaro suka gayyace ta.

An nuna mata hoto da kayan makarantar Hanifa inda ta ce ta gane su.

Haka Kuma masu gabatar da kara sun gabatar da wasu jami’an ’yan sanda biyu – Lurwanu Ibrahim da M. Yanfa a matsayin shaidu wadanda su ne suka dauki jawaban wadanda ake zargi.

Ana dai tuhumar Abdulmalik Tanko da Hashim Isyaku da Fatima Jibril Musa da laifin hadin baki da yin garkuwa da boyewa da kuma kisan dalibarsa Hanifa Abubakar ’yar kimanin shekaru biyar da haihuwa.

Alkalin kotun, Mai shari’a Usman Na’abba ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 9 da 10 ga watan Maris, domin ci gaba da sauraron karar.