✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Hanifa: Kotu ta daure budurwar Abdulmalik Tanko shekara 2

Kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko da Hashimu Isyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotu ta yanke hukuncin daurin shekera biyu a gidan yari ga Fatima Jibril, budurwar Abdulmalik Tanko, wanda ya kashe dalibarsa mai shekara biyar, Hanifa Abubakar.

Kotun ta yanke wa Fatima hukuncin ne a ranar Alhamis, tare da Abdulmalik da abokinsa Hashimu Isyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa laifin sacewa da kashe Hanifa.

“Wadda ake zargi ta uku (Fatima Jibril) kuma a matsayinta na uwa an yanke mata hukuncin daurin shekara daya kan laifin yunkurin garkuwa da wani shekara daya kuma saboda hadin baki,” inji alkalin kotun.

Mai Shari’a Usman Na’abba, ya kuma yanke wa Abdulmalik karin daurin shekara biyar a gidan yari, shi kuma Hamisu karin daurin shekara uku a kurkuku.