✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanifa ta Biyu: Yadda makwabci ya sace tare da kashe ’yar makwabcinsa

Abin da takaici ganin yadda wannan yarinya take kiran wanda ake zargin da Baba.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce, al’ummar Sabon Garin Narabi da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi suka wayi gari da juyayi da alhini, sakamakon gano gawar wata yarinya ’yar shekara hudu mai suna Khadija Abdullahi da ake zargin makwabcinsu mai suna Alhaji Kabiru Abdullahi ya yi garkuwa da ita, kuma bayan ya karbi kudin fansar Naira dubu 150, ya hallaka ta, ya binne gawar ta a sabon gidan da ya gina.

Da yake yi wa wakilimu bayani kan yadda wannan abin jimami ya faru, mahaifin yarinyar mai suna Malam Abdullahi Yusuf, ya ce bai taba tunanin cewa wannan mutum zai aikata wannan abin bakin ciki ba.

Ya ce domin mutumin, shi ne ya yi masa hanyar sayen filin da ya gina gidan nasa da yake ciki. Kuma duk kayan ginin gidan nasa a gidan wanda ake zargin ya rika ajiyewa, har ya kammala gina gidan shekara bakwai da suka gabata.

Malam Abdullahi Yusuf ya ce ’yar tasa ta bace ne a ranar Laraba, azumin bana yana kwana 16.

Ya ce a ranar ya tafi kasuwa sai iyalansa, suka kira shi a waya suka sanar da shi, cewa ba a ga yarinyar ba.

“Bayan kwana daya, na kai rahoto ofishin ’yan sanda, kuma har aka kai kwana bakwai, babu labarin wannan yarinya.

“A kwana na takwas ne sai aka zo aka soka wata wasika a kofar gidana. Da na bude wasikar sai na ga an rubuta cewa kada ka yi mamaki, mu ne muka yi garkuwa da ‘yarka. Muna neman kudin fansarta Naira miliyan daya,” inji shi.

Abdullahi Yusuf ya ce bayan mako biyu, sai aka sake turo masa sako ta waya, cewa “Ka yi kokari ka karbo fansar ’yarka, idan kuma har ba ka yi kokarin fanso ta ba, ruwan sama yana nan yana dukanta a wajen da muka ajiye ta.

“Idan ka bari ta mutu, kai ma kana da kamashon alhakin da za a dauka.”

Mahaifin yarinyar ya ce da ganin sakon, sai ya kira su a wayar da suka turo sakon ya ce nawa za a ba su? Sai suka ce ya ba su Naira dubu 300.

Sai ya ce masu gaskiya ba ya da kudin. Sai suka ce to nawa zai bayar? Sai ya ce masu zai bayar da Naira dubu 50.

“Da suka ji haka, sai suka hau ni da zagi. Sai na ce to zan ba su Naira dubu 100, sai suka ce in bayar da Naira dubu 200. Na ce zan ba su Naira dubu 150, sai suka yarda a haka.

“Suka ce in kai kudin bayan wani gidan bolo a nan garin Narabi a gindin wata bishiyar dorawa. Na je na kai kudin, kamar yadda suka ce. Suka je suka dauka, kuma suka ce da karfe biyu na rana, za su dawo mani da ’yarta,” inji mahaifin.

Abdullahi ya ce har gari ya waye, ba su dawo masa da ’yar ba, sai ya rubuta masu sako ta wayar cewa kun ce za ku dawo mani da yarinya, amma har yanzu ban gan ta ba. Sai suka ce kada ya dame da su.

Ya ce har kusan Karamar Sallar nan da ta gabata, ba su dawo masa da yarinyar ba. Abdullahi Yusuf ya ce an yi ta addu’o’i a masallatai a lokacin azumin kan Allah Ya fito da yarinyar.

“Ana yi Karamar Sallah da kwana uku, sai suka kara turo mani sako ta waya, cewa idan ban kara tura masu da Naira dubu 150 ba, har abada na rabu da wannan yarinya.

“Nan take hankalina ya tashi, suka ce in kira su washe gari da safe. Da na kira su sai suka kama zagina, shi ne da na tunzura sai na ce ku ba mutanen kirki ba ne,” inji shi.

Mahaifin yarinyar, ya ce daga baya an fara zargin makwabcin nasa, domin da wannan abu ya faru, sai ya tashi daga gidan da suke makwabtaka, ba tare da ya fada masa ba, ya koma sabon gidan da ya gina.

Ya ce sai aka fada wa jami’an tsaro na Civil Defence, suka je suka kama shi a sabon gidan nasa yana kokarin ya gudu.

Ya ce da jami’an tsaron suka tambaye shi, me ya sa yake kokarin gudu? Nan take ya ce asirinsa ya tonu.

“Daga nan jami’an tsaro na Civil Defence suka tafi da shi ofishinsu suka tambaye shi ina yarinyar da ya dauka? Nan take ya ce sun kashe ta, sai suka tambaye shi ina gawarta? Sai ya ce sun jefa ta a ruwa.

“Daga nan sai suka wuce da shi Bauchi. A can ma da aka tambaye shi, ya ce sun jefa ta ce a ruwa,” inji shi.

Abdullahi Yusuf ya ce bayan da suka dawo gida, suka yi shawara suka ce su kara komawa a kara tambayarsa wajen da suka kai yarinyar nan domin wajen da ya ce sun jefa ta a ruwa, an duba babu alamarta.

Ya ce da suka koma jami’an tsaro na Civil Defence suka fito da shi gabansu, suka ce ya fadi gaskiyar wajen da ya kai yarinyar nan.

“Ya ce lallai sun jefa ta a ruwa ne. Da jami’an tsaron suka matsa shi, sai ya ce zai fadi gaskiya. Ya ce sun kashe yarinyar ce suka binne a sabon gidansa. Ya yi bayanin wajen da suka binne ta a cikin gidan.

“Da muka dawo aka duba gidan, aka tone wajen da ya yi bayani, sai aka samu gawar yarinyar ya dukunkune ta, ya sa a buhu, ya daure wuyanta sai da aka sa wuka aka yanken buhun, aka fito da ita aka sanya ta a likafani, aka je aka yi mata jana’iza,” inji mahaifin yarinyar.

Ya ce kafin a ga gawar yarinyar, hankalinsa yana tashe amma da ya ga gawar sai hankalinsa ya kwanta.

“Kafin a gano gawar yarinyar nan na kai kwana biyar ba na iya cin abinci.

“Amma a ranar da aka gano gawarta, sai na ji na samu natsuwa har na ci abinci. Wannan mutum shi da yarana sun shaku sosai, wani lokaci sai in zo insame su suna wasa da shi a kofar gida.

“Wannan yarinya ta san shi sosai kuma suna wasa. A ranar da suka tashi daga wannan gida da yake makwabtaka da mu, sai da ’ya’yansa suka yi barci a cikin gidana,” inji shi.

Abdullahi Yusuf ya ce su biyu ne suka yi wannan aika-aika. Kuma dayan yana garin Nabardo ne da ke karamar hukumar, kuma shi ne ake zargi yana canja murya yana magana da shi.

Ya yaba wa jami’an tsaro na Civil Defence kan kokarin da suka yi wajen gano gawar yarinyar da kuma wadanda ake zargi da wannan danyen aiki.

Kuma ya yi kira ga hukuma, kan ta yi wa wadanda ake zargin tsattsauran hukumci, domin ya zama darasi ga masu miyagun halaye irin nasu.

Da take zantawa da wakilinmu kan al’amarin, mahaifiyar yarinyar mai suna Maimuna Abdullahi ta ce a ranar da aka dauke yarinyar, tana kofar gida suna wasa da ’yan uwanta.

Ta ce “Gaskiya ban taba tunanin wannan mutum zai yi mana wannan cin amana ba, saboda yadda muke da iyalansa. Abin da takaici ganin yadda wannan yarinya take kiran wanda ake zargin da Baba.

“Babu abin da zan ce, sai dai in ce na bar shi da Allah. Ita kuma ina rokon Allah Ya yi mata rahama.”

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil, don jin ta bakinsu kan wannan al’amari, ya shaida wa wakilinmu cewa har zuwa lokacin jami’an tsaro na Civil Defence ba su mika masu al’amarin ba.