✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanifa: Yadda aka tozarta amana saboda abin duniya

A ’yan shekarun da ba su wuce 40 ba, al’ummar Arewa ba mu san wadannan musifu ba.

A wannan makon cikin kaduwa da jimami tare da nannauyar zuciya ni GIZAGO (08065576011) nake gabatar da wannan tsokaci, wanda ya danganci abin takaici da rashin imani da wani karkataccen mutum mai suna Abdulmalik Tanko ya aikata a Kano.

Mutumin da ya jagoranci cin zarafin dalibarsa, ya yi garkuwa da ita domin amsar kudin fansa amma daga karshe ya kashe ta, ya daddatsa gawarta, ya binne ta a harabar makarantar.

Wannan mummunan al’amari yana ishara da yadda karshen zamani ya haifar da masifu da birkitattun al’amura, inda dan Adam ya kekashe zuciyarsa, ya shafa wa idanuwansa toka, babu tausayi da jinkai, babu gaskiya babu amana, duk domin neman dukiya ido rufe.

A wannan zamani, labaran takaici da cin amana da rashin jinkai sun sha faruwa a wannan zamani namu.

Abdulmalik Tanko tare da sauran mutum biyu da ake zargin hannunsu a kisan Hanifa

An samu inda da ya hada baki da masu garkuwa da mutane suka kama mahaifinsa domin amsar kudin fansa. An samu inda mahaifi ya yi wa diyarsa fyade. An samu inda kane ya zambaci yayarsa, kamar kuma yadda makwabci ya hada kai da barayi suka yi wa makwabcinsa fashi.

Shin wai mene ne dalilin da ya haifar da wannan mummunan yanayi a kasar nan, musamman ma a yankinmu na Arewa, inda muke da kyawawan al’adu da dabi’u, muke da kyawawan addinai da kuma bin addinan sau da kafa?

A ’yan shekarun da ba su wuce 40 ba, al’ummar Arewa ba mu san wadannan musifu ba.

Fashi da makami, garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa da zamba cikin aminci da damfara, duk sai dai mu ji labarin suna faruwa a wasu sassan duniya ko kuma a Kudancin Najeriya.

Amma a yau abin ya rikide, mutum mai Sallah biyar a rana, amma shi ke jagorancin ta’addanci da cin zarafin ’yan uwansa. Ta ina muka faro kuma me ya haddasa mana wannan mummunan yanayi?

Gaskiya ne abin da aka ruwaito daga Manzon Allah, Muhammadu (SAW), wanda ya bayyana cewa a karshen duniya al’amura za su hargitse, zunubbai za su yawaita, tashe-tashen hankali za su yawaita, cin amana da shedananci za su watsu a bayan kasa, al’umma za ta rasa aminci.

Kisan Hanifa Abubakar
Hanifa Abubakar, yarinyar da aka gano gawarta a Kano

Manzo ya ce lokaci zai zo, inda kashe-kashe za su yawaita, inda za ta kai ga mutum ya yi kisa, amma shi bai san dalilin aikata haka ba, haka shi ma wanda aka kashe bai san laifin da ya aikata aka kashe shi ba.

Annabin ya ce zamani zai so saboda rikicewar al’amura, mutum zai kalli kabari ya ce da ma shi ne a cikinsa.

Ga shi dai mun samu kanmu a wannan mummunan yanayi, inda rikicewar al’amura ta kai gargara. Babu adalci da gaskiya da jinkai a shugabanci.

Babu jagoranci na kirki a cikin iyali, babu zumunci da ’yan uwantaka, babu hadinkai da zaman fahimta a cikin unguwanni da garuruwa.

Babu kishin kasa babu tsaro sai tsoro, inda jami’an tsaro suke jefar da amanar aikinsu, suke zama masu samar da barazana da tsoro ga al’umma, maimakon tsaro.

Al’umma ta koma daraja mai kudi ko da asharari ne, ba a daraja mai daraja domin bai da dukiya.

Addini da malaman addini sun koma yin tarayya da ha’inci da maha’inta. Aure ya zama jidali da neman jari, tarbiyya ta koma gidajen talabijin da finafinai.

Shari’a ta zama sai mai dukiya, mara kudi komai gaskiyarsa ba zai samu adalci ba. Wannan yanayi da al’ummarmu ta shiga, ita ta haifar da mutane marasa imani kamar Abdulmalik Tanko da matarsa da bazawararsa da abokinsa, wadanda suka yi tarayya wajen halaka yarinaya Hanifa.

Don haka, ya zama wajibi ga hukumominmu da su gaggauta hukunta wadannan tantiran mutane. Idan kuwa shari’a ta yi sakaci a hukunta su, to tabbas an share hanyar afkuwar bala’o’i a cikin al’umma.

Rashin hukunta su zai sanya al’umma su rika daukar hukunci a hannunsu. Babu shakka Abdulmalik ya ci amana, kasancewarsa shugaban makarantarsu marigayiya Hanifa.

Ya kamata a ce shi ne kan gaba wajen bayar da kariya da tsaro ga yara, amma duk ya jefar da wannan kima ta shugaba kuma uba, wanda shi ma yake da ’ya’ya irin Hanifa.

Haka ita ma matarsa, ba ta kyauta ba ko kadan, kasancewarta uwa, wacce ya kamata a ce ta tona wa mijin nata asiri, domin ceton ran wannan yarinya.

Shi kuwa abokin Abdulmalik ya ci amana, musamman da ya biye wa son zuciya, ya taimaka wajen haka ramin binne wannan yarinya.

Allah Ya jikan Hanifa, ya ba iyayenta da danginta da mu sauran al’umma hakuri. Allah Ya kara tona asirin maha’inta, maciya amana, ’yan ta’adda irinsu Abdulmalik Tanko.

Allah Ka shiryar da mu, ka kiyashe mu da fadawa cikin aikata muggan ayyuka, amin!