✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hankalina ba zai kwanta ba sai na gaji Buhari a 2023 — Yahaya Bello

Gwamnan ya bayyana kudurinsa na son maye kujerar shugaba Buhari a 2023.

Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya bayyana aniyarsa ta gadar kujerar Shugabancin Kasar nan, da zarar shugaba Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa a 2023.

Ya bayyana haka ne a wata tattaunawarsa ta musamman ranar Litinin da gidan talabijin na Arise.

A cewarsa, yana da dukkanin wata nagarta da ake nema a wajen Shugaban Kasa.

“Da yardar Allah ba zan samu sukuni ba har sai an rantsar da ni a ranar 29 ga watan Mayun 2023, a matsayin magajin Shugaba Buhari,” inji shi.

Kazalika, ya yi karin haske kan yanayin da samu Jihar Kogi bayan zama gwamna a 2016.

Ya ce, “Na gaji jihar nan lokacin da take tsaka da miyagun ayyuka

“Don haka na yi aiki tukuru wajen gina tare da shigar da matasa da mata cikin gwamnatina.

“Amma yanzu Kogi ta samu ci gaba mai tarin yawan gaske, wanda na daga cikin irin ci gaba da kasa ke so ta samu,” cewar Yahaya Bello.