✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hansi Flick ya zama sabon kocin Jamus

Flick zai ke daukar Fam miliyan 6.5 a shekara, kasa da albashinsa a Bayern Munich.

Kasar Jamus ta tabbatar da daukar kocin Bayern Munich, Hansi Flick a matsayin wanda zai maye gurbin mai horas da ’yan wasanta, Joachim Low, da zarar an kammala gasar cin kofin Euro 2020.

Bayan ajiye mukaminsa, Flick zai dauki gabarar jagorantar tawagar ’yan wasan kasar Jamus.

Jamus ta fitar da sanarwar daukar sa ne a ranar Talata, inda ya rattaba hannu na tsawon shekaru uku, zuwa karshen kakar wasanni ta 2024.

Flick, zai ke daukar Fam miliyan 6.5 a duk shekara, kasa da abin da yake dauka a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich.

Tun kafin kakar wasanni ta bana ta kare, bayan sanar da cewar zai bar Bayern Munich aka shiga yada jita-jitar zai karbi aikin horas da tawagar kasar Jamus.

Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona Joan Laporta, ya jima yana zawarcin Flick domin ya karbi kocin Barcelona.