Hanyar makabartar Damaturu | Aminiya

Hanyar makabartar Damaturu

Don Allah ku ba ni dama in yi kira ga Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni, kan aikin shimfida kwalta daga hanyar zagaye zuwa makabartar Na-Yi-Nawa. Domin tunda tsohon Gwamna Ibrahim Gaidam, ya bada umarnin shimfida hanyar,  kamfanin da ke aikin ya zuba birji, kawo yanzu bai kara waiwayar hanyar ba. Idan aka yi ruwan sama ana shan wahala wajen wucewa da gawa zuwa makabartar. Saboda haka muna kira ga Gwamna Buni ya sa a kammala hanya mai wacce ba ta wuce kilomita daya ba.

Daga Idriss M Idress Damaturu Jihar Yobe, 08034787886

 

Yanzu al’ummar  Yobe suka san da Hukumar SEMA

A yau ina so in yi jinjina ce ga Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dokta Mohammed Goje game da ayyukan bada agaji da hukumarsa take yi a duk fadin jihar. Hakika yanzu ne al’ummar Jihar Yobe suka san da hukumar, domin da zarar wani bala’i ya samu  a jihar, jami’an hukumar sukan shiga kowane lungu da sako domin tallafa wa wanda abin ya shafa. Haka ma hukumar tana bai wa tsofaffi gajiyayyu tallafi. Kafin zuwan wannan shugaba wannan hukumar dama aikin sa ne bai wa marasa galihu da marasa karfi tallafi. Kuma Mai girma Gwamna Mai Mala Buni ya yi amfani da cancantarsa ya ba shi wannan matsayi. Hakika an ajiye kwarya a mazauninta muna addu’a Allah Ya dafa wa shugaban Ya kara ba shi ikon sauke nauyin da aka dora masa.

Daga Sa’idu Abdullahi Damaturu. 08032127482

 

Maraba da gadar Ibi

Assalam Editan Aminiya. Da fatar kowa yana cikin koshin lafiya amin, a gaskiya na yi matukar farin cikin da na karanta labarin gadar Ibi. Allah Ya tabbatar da alheri amin.

Daga Saminu Artillery Yelwa Shendam Jihar Filato, 08032436477, 08027091994

 

Kira ga Gwamnatin Kano

Assalamu alaikum Editan Aminiya. Ina kira ga Gwamnatin Jihar Kano ta dubi hanyar da ta taso Rimin Gado Jili zuwa Gulu.

Daga Abdurahman Saminu Jili Rimin Gado Kano 08038437323

 

Shawara kan cire tallafi

Salam. Ya kamata Baba Buhari ya janye maganar cire tallafi ko kara haraji a kan abinci ganin abin kan talakawansa zai kare. Maimakon haka a cire na kananzir  mana. A huta lafiya.

Naka Baban Larai Loko, ABS  07053876024

 

Kira ga Gwamnatin Sakkwato

Assalamu alaikum. Don Allah Edita ka ba ni dama in isar da sakona ga Gwamnan Jihar Sakkwato kan rashin biyan kudin jarrabawar kammala makarantar sakandare (WAEC da NECO). Ya tuna cewa, ba nan ne matabbata ba kuma ya tuna da hakkin talakawa na kansa.

Daga Mujaheed M. Hadi Gobeer S 08127514757

 

Jinjina ga Gwamnan Katsina

Salam. Fatan alheri ga Gwamna Aminu B. Masari bisa kokarinsa na ganin an samu zaman lafiya a jiharmu. Allah Ka azurta jiharmu da kasarmu da zama lafiya, amin.

Daga Dahiru Dauda (KGY) Bindawa. 08030693021

 

Daliban Jigawa sun gaji da gafara sa

Assalamu alaikum. Fatan alheri marar adadi ga daukacin ma’aikatan jaridar Aminiya mai albarka. A ba ni dama domin in yi kira ga Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar Talamiz kan ya taimaka ya biya daliban jihar kudin ‘scholarship’ dinsu kamar yadda aka saba bayarwa duk shekara, lura da  cewa tun wata uku aka kammala tantance mu amma har yanzu shiru muke ji kamar an shuka dusa. Daga karshe nake fatar Mai girma Gwamna zai duba wannan koken namu da idon basira.

Daga Mutawakkil Gambo Doko, Karamar Hukumar Garki, Jihar Jigawa. 07032695589

 

Don inganta ilimi

Salam Edita. Don Allah ka isar min da kokena ga Gwamnan Jihar Kano wajen sanya tallafi ga dakin karatu na jihar don zamanantar da dakin karatun a yanzu.

Daga Mamuda Abdullahi 08036823926

 

Taya murna ga Zamfarawa

Assalam Edita. Ina taya Gwamna Bello Matawalle murnar cikarsa kwana 100 a kan mulki mun ga ci gaba a Zamfara Allah Ya taya ka riko.

Daga 08161788025

 

Kira ga Hukumar Kwastam

Assalam Aminiya da fatar kuna lafiya. Edita don Allah ku tura min sakona ga Hukumar Kwastam kan matakin cin amanar ’yan kasuwa da suka dauka a Jihar Katsina. Gaskiya ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin hana faruwar haka nan gaba saboda tabbatar da tsaro.

Daga Babangida Jikan Mani, Sabo, Yaba Legas 09031366660

 

Ina bukatar addu’arku

Fatan alheri gare ku amintacciyar jaridarmu mai farin jini. Edita ka taimaka min ka ba ni dama domin in sanar da ’yan uwa da abokan arziki cewa, a ranar Lahadin da ta gabata aka daura aurena, a Unguwar Ayagi da ke Kano, don haka ina neman addu’o’in mutane, musamman ma’abota karanta jaridar Aminiya, don samun zaman lafiya da karuwar arzikin zuriya tagari, amin.

Daga Murtala Ahmed Abubakar Kwalli Gidan Doki Kwalli, Kano, 07068295953

 

Zamfarawa sun ga canji

Jinjina ga Gwamnan Zamfara, Zamfara mun ga canji sosai. Saboda ga shi bana kowa ya yi noma a gonarsa ba tsoro ba fargaba. Allah Ya kara kare mu amin.

Daga Muhammad Danbawa Gadar Zaima Bukkuyum, 07053407125.

Ta’aziyyar Bashir Sama’ila Ahmed

Ina isar da ta’aziyyata zuwa ga iyalai da ’yan uwa da abokan arziki kan babban rashin dan jarida Bashir Sama’ila Ahmed. Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa amin summa amin.

Daga Usman Maniya, 08057129100

 

Mun yaba da jajircewar Shugaba Buhari

Edita don Allah ka ba ni dama in yi jinjina ga Shugaban Kasa Buhari. Mun gamsu da jajircewar da kake yi wajen ganin Najeriya ta kai tudun-mun-tsira. FatarmuAllah Ya kara kiyaye ka Ya kara maka lafiya, Ya kuma kau da idon marasa kishin kasa a kan gwamnatinka, Ya kuma ba mu damina mai albarka, amin.

Daga Haladu Ahmadu Chibiyayi Zaki Jihar Bauchi, 08030703952

 

Ga Dan Majalisar Gwarzo

Salam Editan Aminiya mai albarka. Don Allah ka taimake ni ka isar min da rokona ga Dan Majalisar Karamar Hukumar Gwarzo Alhaji Inusa Kayu da ya yi wa Allah da Annabi ya gyara wutar lantarkin garin Sabon Layin Kara da Hawan Ganji da Dan Tasau da Kara da Lahadi da Getso da Gidan Dandawa da Dalangashi domin jin dadin rayuwar jama’a.

Daga 09023489162

 

Ta’aziyyar Bashir Musa Liman

Mun yi rashin jan gwarzo dan uwanmu Musulmi wato Bashir Musa Liman. A madadina da iyalina muna yi wa jama’ar Jama’are da Jaridar Aminiya ta’aziyyar marigayi Bashir. Allah Ya jikansa da gafara Ya sa haske a cikin makwancinsa, amin.

Daga Tasi’u M. Sani Tashan Nana Argungu, 08062236122

 

Kira ga malamai da shugabanni

Assalam Edita. Ina yi mana fatar alheri. Don Allah ka isar min da sakona zuwa ga malamai da shugabanni su yi hakuri su ci gaba da yin kira ga mutane su nemi  abin da suke nema a wajen Allah ba mutum ba. Yadda ake kashe Musulmi a kasar nan wadansu ma a kona gidajensu a kore su a raba uwa da danta a raba mata da miji wadansu ma ba a san halin da suke ciki ba, yanzu don Allah masu wannan mammunar ta’asa ba sa tunanin Allah Ya kama su?

Daga Auwalu Wali Karofi Bauchi 07031368115

 

Ga talakan da ke rigimar siyasa

Assalam Edita, ka ba ni dama in yi kira ga talakan da yake sanya kansa a cikin rigimar siyasa a kashe shi a banza. Ya kamata ya kiyayi haka, domin ba wata riba zai samu ba

Daga Salisu Chiyaman Too Ligeta Diko Gurara jihar Neja 0805677628

 

Taya Sarkin Hadeja murnar cika shekara 17 a sarauta

Assalamu alaikum Edita. Ina son ka ba ni dama in taya Mai martaba Sarkin Hadeja Alhaji Adamu Abubakar Maje, (CON), murnar cika shekara 17 a gadon sarauta. Hakika Mai martaba ya bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban masarautarsa da Jihar Jigawa da kasa baki daya a cikin wadannan shekaru da ya yi yana mulkin kasar Hadeja. Kuma gain yadda ya rike al’ummarsa da daraja ne mu ma talakawansa muke taya shi murna. Allah Ya karo shekaru masu albarka.

Daga Daddy Bala Kakaburi Hadeja. 07065141489