✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hanyoyi 6 na kare motarka a loackin damina

Ga wasu hanyoyi da za su taimaka wajen kula da ababen hawansu a lokacin damina

Damina lokaci ne na ruwan sama, wanda hakan kan takai walwala da lokutan shakatwar jama’a.

A Najeriya, damina ta fi karfi ne tsakanin watan shida zuwa watan tara duk shekara.

Akan kuma fuskanci wasu kalubale sakamakon shigowar yanayin, kamar ambaliya wadda ke yawan aukuwa saboda rashin kyawawan magudana ruwa da sauransu.

Bisa wadannan dalilai da makamantansu, yana muhimmanci kowa ya kula da zirga-zigarsa a wannan lokaci na damina musamman kuma a idan yana tuki.

Ga wasu hanyoyi da za su taimaka wajen kula da ababen hawansu a lokacin damina kamar haka:

Hasashen Yanayi

Hasashen yana taimakawa wajen sanin yadda yanayin yini zai kasance.

Masana wannan fannin kan duba sannan su auna yadda yanayin yini zai kasance don amfanin jama’a.

Wani lokaci hasashen nasu kan nuna za a samu hazo ko ruwa da iska ko yiwuwar samun ambaliya da makamantansu.

Hakan kan taimaka wa jama’a sanin yadda za su yi shige da fice da abubuwan hawansu a yini. Don haka, sai a kula.

Wurin ajiye mota

Idan ba fita za ka yi da mota ba, to abu mafi kyau shi ne ka rika barin motarka a cikin gareji kowane lokaci.

Ko kuma ka rika amfani da babban mayafin rufe mota wajen kare ata daga dukan ruwa.

Yawan dukan ruwa na illa ga mota saboda sinadarin da ke kunshe cikin ruwan sama, don haka sai a kiyaye wannan.

Injin mota

A yanayi na ambaliyar ruwa a lokacin damina, a rika kokarin kiyaye muhimman sasan mota, kamar salansa da injin da sauransu, kada ruwa ya shiga ya lalata.

Idan kuma aka hango aukuwar ambaliya a lokacin da ake tsaka da tafiya, mafi alheri shi ne a sake hanya.

Idan kuwa babu makawa sai an bi ta cikin ruwan, sai a raba ta gefe, kada a shiga wuri mai zurfi. Don haka a lura da wannan sosai.

Shimfidar mota

Tafiya da karin shimfidar kasar mota yana da muhimmanci don tabbatar da tsaftar cikin mota, musamman a wurare masu tabo, idan wadda ake amfani da ita ta yi datti, sai a sake wata, saboda barin datti a mota na yi wa abin hawa illa.

Kuma amfani da shimfidar mota ta roba ya fi saukin sha’ani, musamman wajen wankewa. Don haka, a kula da tsaftar mota.

Tuki da kulawa

Yayin da ruwan sama ya cim maka kana tuki, yana da kyau ka ba da tazara tsakaninka da motar da ke gabanka don kauce wa aukuwar hatsari.

Saboda tuki cikin ruwan sama, kan sanya gilashin mota dishi-dishi ba a iya ganin da kyau yadda ya kamata.

Haka nan, a tabbatar waifa tana aiki don taimaka wa direba wajen share masa gilashi, sannan a guji yin amfani da matacciyar taya lokacin damina. Da fatan za a kula.

Feshin Silicon

Feshin Silicon maiko ne da ake sanya wa sassan mota don kariya.

Ruwan sama kan yi sanadiyar lalacewar wasu sassan mota wadanda suke a fili, amma amfanin da wannan feshin kan takaita faruwar hakan.

Ya kamata direba ya sani cewa wannan feshi na da muhimmanci ba a damina kadai ba, har ma da lokacin zafi. Don haka, sai a kiyaye.