✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin da za a bi don magance matsalar tsaro — Janar Kukasheka

Kusan ko’ina akwai matsalolin tsaro wadanda suka addabi jama’a.

Tabbas Najeriya tana cikin tsaka-mai-wuya dangane da yadda matsalar tsaro ta ta’azzara. Gabas da Yamma, Kudu da Arewa, maganar ke nan ta sukurkucewar harkar tsaro.

Aminiya ta tattauna da kwararren masanin harkokin tsaro, kuma tsohon Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya, Sarkin Yakin Kanwan Katsina, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya).

Janar din ya yi fashin baki dangane da kalubalen tsaro a Najeriya, ya ba da shawarwarin yadda za a shawo kan matsalolin, musamman barazanar da Kungiyar IPOB, mai nema ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Biyafara.

Ya nemi Gwamnatin Najeriya ta yi hanzarin neman kasar Birtaniya ta mika mata Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, a dawo da shi Najeriya domin hukunta shi.

Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ranka ya dade, al’amuran tsaro na fuskantar barazana iri-iri, ga ’yan Boko Haram, ga ’yan bindiga masu garkuwa domin kudin fansa, ga kuma masu kokuwar neman raba kasa.

Ko za ka yi mana fashin baki kan wannan al’amari?

Assalamu alaikum wa rahamatullah! Tabbas kasar nan tana fuskantar kalubale ta fuskar tsaro ta kusan ko’ina.

Kusan a ce babu wani sashi na kasar nan da ba a fama da matsalar tsaro. Misali, Arewa maso Gabas akwai ta’addanci na ’yan Boko Haram da ’yan uwansu ’yan ISWAP.

A Arewa maso Yamma kuma akwai sata da garkuwa da mutane da matsalar ’yan bindiga dadi, fyade da kashe-kashe da satar dabbobi.

Kudu maso Yamma, ita ma tana fama da matsalar fashi da makami, rikicin manoma da makiyaya, aikata miyagun laifuffuka ta kafafen sadarwa na zamani, kungiyoyin asiri, rikicin kabilanci da kuma son raba Najeriya.

Haka kuma Kudu maso Kudu akwai satar mutane, fashi da makami, sata da fasa bututun mai da makamantansu.

Kudu maso Gabas akwai matsalar fashi da makami, rikicin ’yan ta’adda da ta’addancin haramtacciyar kungiyar masu neman kafa kasar Biyafara, wanda ya kai ga kai hare-hare ga ofishin ’yan sanda da gidajen yari da kuma jami’an tsaro har ta kai ga kashe wadansu daga cikinsu, musanman ’yan sanda.

Arewa ta Tsakiya ba ta tsira ba, domin akwai matsalar tsaro ta sata da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, rikicin makiyaya da manoma da kuma matsalar ’yan bindiga dadi.

A takaice, kusan ko’ina akwai matsalolin tsaro wadanda suka addabi jama’a.

Don haka ana bukatar a shawo kansu, in har ana so tsaro ya inganta yadda ’yan kasa hankalinsu zai kwanta, duk da dai gwamnati da jami’an tsaronta na bakin kokarinsu, a gaskiya sai an tashi tsaye sosai.

A kwanakin baya an samu rahoton mutuwar Shekau. Me wannan yake nufi dangane da batun ’yan Boko Haram?

Abin farin ciki ne da murna ganin cewa wannan shahararren shugaban ’yan ta’adda na Boko Haram ya mutu.

Mutuwarsa ta nuna cewa kamar yadda ake zato, cewa kansu ba a hade yake ba, domin ba su kan turbar gaskiya.

Kuma duk dan ta’adda, karshensa ke nan ko-ba-dade-ko-bajima.

Bayan haka, wannan ya samu nasaba ne bisa kokarin jami’an tsaron Najeriya, musamman sojoji.

Yanzu abin da ya kamata shi ne, sojojin Najeriya da na makwabta su maida hankali su dada kaimi domin su ci gaba da wargaza su, domin idan ba a maida hankali ba, Kungiyar ISWAP za ta yi amfani da damar, ta kara karfi da ci gaba da barna.

Amma kamar yadda muka gani, cewa Abu Mus’ab ya kashe wadansu na hannun damar Abubakar Shekau, ina ganin har yanzu akwai sauran rikici a tsakaninsu.

Don haka sai a ci gaba da far musu kafin su farga.

Wadansu na ganin cewa bangaren Albarnawi zai maye gurbin bangaren Shekau, har suna ganin kamar wannan ya fi Shekau hadari. Me za ka ce?

Ka san shi dan ta’adda ba ya barin abin da ya sa gaba har sai an hana shi.

Ta iya yiwuwa cewa hakan ne, amma ba wani abu ne da zai gagara ba, muddin in aka ci gaba da yakarsu da kuma zakulo miyagun mutanen da ke goyon bayansu, ta ba su bayanan sirri da duk wata gudunmawa, wadanda kullum suna cikin al’aumma.

An samu sauyin Babban Hafsan Sojin Kasa, a sanadiyyar hadarin jirgi da ya samu marigayi Janar Ibrahim Attahiru. Yaya kake ganin kalubalen da sabon Babban Hafsan zai fuskanta a fannin tsaro?

A gaskiya akwai aiki a gabansa, domin an nada shi a cikin wani mawuyacin hali na matsalar tsaro a kasar nan kuma akwai dogon buri daga jama’a.

Kuma bai samu damar karbar jagoranci daga wanda ya gada ba, domin Allah Ya yi masa rasuwa, ba kamar sauran ba.

To, ka ga akwai wasu abubuwa da ba zai sani ba, domin wannan dalili, sai dai shi sabon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Manjo Janar Faruk Yahaya, mutum ne wanda ya san makamar aiki, kuma kwararre ne sosai; domin ya yi aiki a wurare da dama kuma ya rike mukamai da yawa a aikin soja.

Don haka ya san makamar aiki sosai. Amma duk da haka, akwai kalubale sosai ta fuskar samar da ingatantu da wadatatttun kayan aiki, taimakon gwamnati da kuma al’ummar Najeriya baki daya.

Sannan kuma kusan ko’ina akwai sojoji suna fama da kokarin shawo kan matsalolin tsaro a kasar nan. Amma na yi imani cewa zai yi bakin kokarinsa, kuma ya ci nasara, domin mutum ne mai hazaka, kuma kyakkyawan jagora ne wanda yake aiki da gaskiya, rikon amana da tsoron Allah.

Najeriya na fuskantar barazanar Yakin Basasa karo na biyu, musamman yadda Kungiyar IPOB ke tada kayar baya a Kudu maso Gabas. Wace shawara za ka ba jami’an tsaro game da haka?

A wannan magana ba ta jami’an tsaro ba ce kawai. Abu ne wanda dole sai gwamnati ta maida hankali sosai ta fuskar tuntubar shugabannin mutane na wancan bangare, sarakunansu, malaman majami’u da masu fada-a-ji.

Da kuma fadakar da mutanen wajen bitar illar wannnan kungiya, musamman matasa. Sannan a inganta jami’an tsaro ta fuskar kara yawansu, makamai, horarwa da kuma kayan aiki.

Gwamnatin Tarayya dole ne ta sa kasar Birtaniya ta mika mata shugaban wannan haramtaciyar kungiya ta IPOB, wato Nnamdi Kanu domin ya fuskanci shari’a a Najeriya.

Dole sai gwamnati ta jagoranci wasu hanyoyi na hada kan ’yan Najeriya.

Ko akwai wasu shawarwari da za ka ba gwamnoni, musamman wadanda jihohinsu ke fuskantar matsaloliin ’yan bidiga, kamar Neja da Kaduna da Zamfara da Sakkwato da Kebbi da Katsina da sauransu?

Ai sun fi kowa sanin abin da ya kamata, domin sun san asali da dalilin wadannan matsaloli na tsaro. Amma abu na farko shi ne, dole ne sai sun hada kai, sun fahimci juna yadda za su san yadda za su yi maganin matsalar. Kamata ya yi su zama bakinsu daya.

Dole ne a kyautata samun bayanai na sirri da inganta aiki, gwamnati ta tabbatar da cewa kananan hukumomi suna aiki. A kuma samar wa matasa aikin yi ko hanyoyin da za su inganta sana’o’insu.

Iyaye da sauran shugabannin al’umma suna da rawar da za su taka wajen tarbiyya da fadakarwa.

A yi maganin shan kwaya da abubuwa masu sa maye sannan dole ne kuma a rika tuntubar jama’a, kuma a inganta jami’an tsaro da sarakuna.

Wadansu na zargin hannun wasu manyan kasashe wajen zuzuta matsalolin tsaro a Najeriya da kasashe masu tasowa. Ina matsayin irin wannan hasashe kuma me za ka ce, a matsayinka na masanin tsaro?

Da wannan, don wannan, amma babu tabbaci. Galibin matsalolin tsaro na Najeriya suna da nasaba ne da wasu matsaloli a kasar nan.

Amma ba za a kau da zargin cewa kasashen da ke kera makamai suna son kasuwa wa makamansu ba. Don haka ba za su so a zauna lafiya ba.

Haka Allah Ya yi mana arzikin ma’adinai, wadanda suke samu cikin sauki idan ana rikici. Misali, zinari da makamantansu a wasu jihohi kamar Zamfara, wanda ake haka a sayar musu araha.

Don haka, kamata ya yi ’yan Najeriya su rufa wa kansu asiri, mu hada kai a yi maganin wadannan matsaloli, domin mu kadai ne za mu iya wa kanmu magani.

Daga karshe, ko akwai wani karin bayani da za ka yi kan yadda za a magance matsalolin tsaro a kasar nan?

A’a, face fatar alheri da kuma kara kira cewa ba wanda zai iya yi mana maganin wannan fitina, face mu da kanmu, amma sai mun hada kai kuma wadanda suke jagorar al’umma su rike gaskiya da amana.

A nema wa matasa aikin yi da tallafa wa sana’o’i. Ubangiji Allah Ya ba mu zama lafiya, amin.