✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hanyoyin Nishadantar da iyali bayan Ramadan

Yin haka zai taimaka wajen kara masu jajircewa.

Kamata yayi a kullum iyaye su saba wa ’ya’yansu tashi da wuri kafin lokacin Sallar Asuba, kamar yadda suke yi a lokacin Ramadan. Yin haka zai taimaka wajen kara masu jajircewa.

Kafin Sallar Asuba: Kafin Sallar Asuba, an so ma’aurata su shirya wani samfurin nishadantarwa don debe kewa har zuwa lokacin Sallar Asuba yayi.

Mafi kyawun abin yi a wannan lokaci shi ne addu’a domin sulusin karshe na dare lokacine na amsar addu’a.

Sai ma’aurata su tsara yadda zai zama abin burgewa ga yara da iyali duka ta yadda kowa zai ji yana sha’awar yin addu’ar.

Misali: Kullum a zabi wata addu’a a yi ta karantawa ana maimaitawa har sai kowa ya haddace ta.

Sannan kullum a zabi wanda zai gabatar da wata addu’a yana fadi ana amsawa.

A fara daga Maigida har zuwa na karshe daga cikin yara. Ana iya zabar addu’o’in da ke cikin Al’kurani, addu’o’in alkunut, addu’o’in safiya da maraice, addu’o’in neman tsari da sauransu.

A samu addu’o’in kammala karatun kur’ani na Malamai daban-daban, kullam a zabi daya a runka kunnawa a rikoda kowa na saurare.

A sa yara zu zauna cikin sahu duk kalli alkibla tare da daga hannuwansu sama, sannan a fara da dan karamin cikinsu a ce ya roki dukkan bukatocinshi wurin Allah a bayyane kowa na saurare suna cewa amin, da haka har azo kan maigida da uwargida.

Za a iya daukar sautin addu’ar kowanne a waya don tuna baya.

Ma’aurata za su iya samar da wani littafi, a yi mashi lakabin littafin addu’a, sai a ba kowa ya rubuta addu’o’insa da bukatunsa wurin Allah, yaran da ba za su iya rubutawa ba a rubuta masu, sai uba ko uwa su rinka karantuwa sauran yara na cewa amin.

Gab da ketowar alfijir kuma lokacine na neman gafara wajen Allah Azza wa Jallah, don haka sai iyali duka suyi ta istingifari gabadaya ko daban daban, amma don kayatar da yara, yafi kyau uba ya runkar yin shi cikin sigar wake yaran na amsawa.

Bayan Sallar Asuba: Ayyukan ibada mafi dacewa bayan gabatar da Sallar Asuba sune karatun Al’kuran, da yawaita fadar kalmomi na na zikrin Allah Madaukakin Sarki kamar su tasbihi, tahmid da sauransu.

Sai ma’auarata su tsara wannan ta yadda zai kayatar da yara su ji suna son aikata su saboda nishadin da ke ciki.

Karatun Kur’ani: Kullum a zabi wata Sura wacce kowa ya iya karantawa, sai iyali duka su rinka yin kira’arta gaba daya a lokaci daya. misali, ana iya farawa daga juz’in Amma a yo kasa.

A zabi wata Sura ta Musamman kullum a haddace Aya daya a cikinta, a yi ta maimata wannan Aya har sai kowa ya haddace ta.

Sai yin musaffa iyali duka, watau maigida ya fara karanto Ayar farko cikin wata sura ta musamman, daga nan sai uwargida ta karanta mai bi mata, da haka har a sake kewayo har zuwa karshen Sura.

Sannan maigida sai ya zama Malami ga Iyalansa, kowanne biya karatunsa na Alkur’ani, ayi masa gyara kuma a kara masa.

Sannan Maigida na iya sa gasa tsakanin yaransa, ya basu wata hadda, duk wanda ya riga haddacewa ayi masa wata babbar kyauta wadda zai ji dadinta sosai cikin zuciyarsa.

Sannan ana iya yin addu’o’in zikrin Allah Madaukakin Sarki, kullum sai a zabi wane zikri na yabo, godiya, kambamawa, daukakawa ko tsarkake Allah Madaukakin Sarki. A yi ta maimaita shi har sai kowa duka ya iya.

Sannan a wannan lokaci sai a gabatar da azkar da addu’o’in neman tsari na safe. Bayan an kammala sai ayi sallar duha sannan kowa sai ya kama gabansa zuwa ga abu mafi dacewa gareshi a wannan lokacin.

Asusun Bayan Ramadan: Yin sadaka da yawan kyauta nasa taushi da malalar farin ciki cikin zuciya, ga kuma lada da budewar kofofin arziki daga Allah Madaukakin Sarki.

Ma’aurata su koyar da diyansu rabuwa da abin da suke so don kwadayin samun lada wajen Allah da karuwar arzikinsu na zahiri da na zuci.

Haka kuma ma’aurata idan sun yi asusun a na son kowa daga cikin yara a kullum zai rinka saka wani abu a cikinsa koda daga cikin kudinsu na makaranta ne, za su rinka cirewa, kuma ranar da ya cika sai a fasa a ba yara su kyautar da shi ga mabukata.

Hakan zai karawa yaran jin tausayin mabukata. Sannan ana iya sa yara su bayar da koda kala daya ne daga suturunsu, sai a hada gaba daya a kyautar dasu ga mabukata ko akai gidan marayu.

Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu dace, ibadun da muka yi a wannan wata mai karewa su zama karbabbu. Kuma Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin