✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin tsabtace hammata a lokacin zafi

Abubuwa da dama ne suke kawo hammata ta yi baki ko da an aske gashin wurin.

Barkanmu da sake haduwa da ku a wannan fili namu na kwalliya.

A yau na kawo muku yadda ake kula da hammata.

Idan an gyara jiki kada a manta cewa akwai inda ya fi muhimmanci da za a kula da shi.

Musamman bayan an aske gashin wurin, akwai hanyoyi da za a bi don hana wajen yin baki. Abubuwa da dama ne suke kawo hammata ta yi baki ko da an aske gashin wurin.

Yawan zufa da amfani da man cire gashin hammata da yawan kiba da kuma amfani da turare mai karfi a hammata. A sha karatu lafiya.

Amfani da man kwakwa: Babban abin da ake amfani da shi a wajen hada man zamani shi ne man kwakwa domin yana dauke ne da sinadaran kara haske kuma yana da bitamin E.

A shafa man kwakwa a hammata kullum a yi minti goma kafin a yi wanka.

Bayan an yi haka, sai a wanke da sabulu marar karfi (wanda sinadaran da aka hada shi ba masu zafi ba ne) da kuma ruwan dumi.

Amfani da gurji da lemon tsami: Kamar yadda aka san cewa ruwan lemon tsami na dada hasken fata, haka ma gurji na dauke da sinadarin kara wa fata haske da kuma sanya ta laushi da sulbi.

A hada ruwan lemon tsami da markadadden gurji a wuri daya sannan a shafa a hammata. A bari ya jima na tsawon minti goma sannan a wanke da ruwan dumi.

Garin kurkum da kwai: Kurkum ma na dada wa fata haske, za a iya kwaba garin kurkum da ruwan kwai sannan a shafa a hammata bayan minti 10 zuwa 15 sai a wanke da ruwan dumi. A yi haka a kullum kafin a yi wanka.

Aski: A daina barin hammata da gashi a yi kokarin aske shi a lokacin da ya fito. Domin idan da akwai gashi a hammata, zai hana gumi bushewa ya yi ta wari.

Sai a ga ko an fesa turare, sai a ji warin turaren daban na hammatar daban.

Yin amfani da wadannan abubuwan wajen gyaran hammata zai rage warin jiki da hana fesowar kuraje da fitowar bakin launi a karkashin hammata da kuma rage gumin hammata.