✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu a gidan haya nake zama a Abuja —Shekarau  

Ina rokon Allah Ya kawo budin da zan gina nawa.

Sanatan Kano ta Tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya ce har yanzu a gidan haya yake zama a Abuja kuma yana addu’ar Allah Ya hore masa ya gina na kansa.

Sanatan wanda ya yi Gwamnan Jihar Kano wa’adi biyu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani ga rahoton cewa, an ba shi Dalar Amurka miliyan 1 domin ya bar Jam’iyyar NNPP.

A bayan nan ne dai dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya tabo wasu zarge-zarge a kan Shekarau, wanda rahotanni ke cewa yana shirin barin jam’iyyar.

Sai dai a yayin da yake jan hankalin mabiyansa, Majalisar Shura da kwamitoci da aka kaddamar kan halin da ake ciki a Jam’iyyar NNPP, Sanatan ya ce ba zai taba cin amanarsu ba.

“Har yau, ba don wani ya ji wannan maganar ba, har yanzu a gidan haya nake zaune a Abuja. Ina rokon Allah Ya kawo budin da zan gina nawa.”

“A shekara 42 na zama na jagora, na yi shugaban makarantar sakandaren GSS Hadejia mai dalibai 500 da malamai 64.

“A wancan lokacin na samu dama da zan iya sanya hannu kan bukatuna kuma a amince da duk adadin kudin da mutum zai iya tunani a kai.

“Kwamishinonina duk suna raye, ban taba zayyana wanda ya kamata a ba wa kwangila ba.”