✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Har yanzu ba a yi wa kashi 80 na ’yan Afirka riga-kafin Coronavirus ba’

Kamfanonin da ke samar da ita sun fi bayar da fifiko ga kasashe masu karfin arziki.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce har yanzu ba a yi wa kashi 80 cikin 100 na mutanen Afirka allurar riga-kafin Coronavirus ko da daya ba.

Shugaban WHO, Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro ta intanet yayin cika shekara daya da kaddamar da shirin samar da rigakafin a duniya da ake kira Covax.

BBC ya ruwaito Dokta Tedros ya ce “kiyasinmu ya nuna cewa riga-kafin da za a samar za ta isa a yi wa dukkanin manya na duniya kuma har a kara yi wa mutanen da ke cikin hadarin kamuwa da cutar sosai zuwa wata uku na farkon shekaran nan.”

Covax shiri ne na tabbatar da raba daidai a tsakanin kasashen duniya wajen samar da riga-kafin Coronavirus.

Shugaban na WHO ya ce shirin ya gamu da nakasu sosai saboda abin da ya kira “kaka-gida” da kasashe suka yi a kan rigakafin da kuma yadda kamfanonin da ke samar da ita suka fi bayar da fifiko ga kasashe masu karfin arziki.