✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu babu wani batu kan ’yan matan Chibok 110 da aka sace

Daga cikin daliban 276, 57 sun yi nasarar kubuta daga hannun mayakan Boko Haram.

Al’ummomi a Jihar Borno sun ce har ya zuwa yanzu babu wani batu kan dalibai mata 110 daga cikin 276 da mayakan Boko Haram suka sace a Sakandaren Chibok a shekarar 2014.

Wata kungiyar da ake kira Kibaku ta raya Yankin Chibok, wadda ke sahun gaba wajen fafutukar ganin an ceto ’yan matan ta hannun shugaban ta Dauda Iliya, ta ce daga cikin daliban 276, 57 sun yi nasarar kubuta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

Iliya ya ce daga shekarar 2012 zuwa yanzu, an kashe mutane sama da 72 a yankin, yayin da aka sace sama da 407, tare da kona gidaje da wuraren sana’oi da majami’u da kayan abinci da kuma sace motoci sama da 20.

Shugaban al’ummar ya ce daga karshen shekarar 2018 zuwa yanzu, mayakan Boko Haram sun tsananta kai hare hare a yankin, ciki har da wanda aka kai Kautikari a ranar 14 ga watan Janairun bana, inda aka sace ’yan mata biyar tare da kashe wasu mutum uku da kuma kona gidaje da majami’u.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito, Iliya ya ce har yanzu suna jiran hukumomin Najeriya su ceto musu dalibai mata 110 da aka sace a shekarar 2014, tare da bukatar kara yawan sojoji da kayan aiki a Chibok domin dakile hare haren da ake kai musu.

Kazalika, Iliya ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kafa sansanin ’yan gudun hijira a garin na Chibok tare da yi wa garin tanadin ababen more rayuwa da sana’o’i domin dogaro da kai da kuma wadatuwa da abinci.