✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Har yanzu ban yanke shawarar zuwa Saudiyya ba —Biden

Biden yana jin cewa Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ba ya bin doka.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce har yanzu bai yanke shawarar ko zai tafi Saudiyya ba, mako guda bayan da bayyana yiwuwar  yin bulaguro.

Majiyoyi sun ce Biden na shirin tafiya Saudiyya, daga nan ya wuce Turai da Isra’ila a karshen watan Yuni.

Fadar White House ta ce shugaban kasar yana jin cewa Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, “ba ya bin doka.”

Bayanai sun ce Biden na yi wa Yariman wannan gani-gani saboda zarginsa da taka rawa wajen kisan dan jaridar Washington Post, Jamal Khashoggi, a Turkiyya a shekarar 2018.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2018 ne Majalisar Dattawan Amurka ta dauki wani irin mataki da ba ta taba dauka ba kan kasar Saudiyya, kawar Amurka ta kud-da-kud, bayan da ta amince da wani kuduri na kawo karshen goyon bayan da Amurka ke bai wa Masarautar Saudiyya don yin Allah wadai da kashe Jamal Khashoggi.