✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Har yanzu harkar kwallon Super Eagles babu armashi’

Tsohon mai horas da kungiyar Super Falcons, Godwin Izilein, ya ce har yanzu babu wani ci gaban a zo a gani da aka samu a…

Tsohon mai horas da kungiyar Super Falcons, Godwin Izilein, ya ce har yanzu babu wani ci gaban a zo a gani da aka samu a tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles karkashin sabon kocinta, Jose Peseiro.

Izilein ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) hakan ranar Laraba, inda ya ce lallasa Sao Tome da Principe a wasan samun tikitin shiga gasar cin kofin Afirka na 2023 ba shi ke nuna ta je inda ake so ba.

Tsohon Kocin ya koka kan rashin sabbin dabaru a filin wasa, inda ya ce kungiyar  na ci gaba da nuna rashin kuzari da kuma taka lamin wasa a kwallayenta.

Izilein ya ce ya gano hakan ne daga yanayin wasa da suka yi karkashin sabon kocin kungiyar da ake sa ran zai kawo ci gaba a kungiyar.

ya ce “Har yanzu ban ga wani sabon abu ba, tsohon salon da muka saba gani na wasa ba kuzari sosai  har yanzu bai sauya ba, Victor Osimhen ne kadai yake kokari a ’yan wasan, sai dai ya na bukatar ’yan wasan da suka iya taka leda mai kyau, wannan dole ne in dai ana son ci gaban kungiyar”, inji shi.

“Ya kamata ’yan wasan su san cewa suna buga kwallo ne a matsayin kungiya ba daidaiku ba, domin har yanzu ba sa taka leda a matsayin kungiya, duk mai kallon wasan ya san wannan, sannan akwai aiki a bangaren kuzari da gudu, da kuma dabarun taka kwallo ga ’yan wasan tsakiyarmu,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa “Wannan zai sa a samu kai harin kwallon mai nauyi da kuma kara karfin ’yan bayan kungiyar.