✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu ina sa ran zan fita Kasar waje — Rabi’u Ali

Gaskiya ba wani ba wani dan kwallon da nake koyi da shi illa Cristiano Ranoldo.

Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars, Rabi’u Ali wanda aka fi sani da Pele fitaccen dan kwallon kafa ne da ya fito daga Jihar Kano.

A tattunawarsa da Aminiya ya ce har yanzu bai fid da rai zai iya samun damar yin wasa a kasar waje ba.

A cewarsa sirrin dadewarsa a harkar kwallon kafa shi ne yin wasa da yake yi ba tare da nuna gajiyawa ko raina wasa ba.

Da sauran batutuwa da suka danganci harkar wasan kwallon kafa

Mene ne takaitaccen tarihinka?

An haife ni a Karamar Hukumar Fagge. Na yi karatun firamare da sakandare a Unguwar Fagge.

Daga nan na koma Unguwar Birged kafin daga bisani na sake dawowa Faggen inda na shiga harkar kwalllon kafa.

Yaya aka yi ka shiga wasan kwallon kafa?

Tun ina yaro na tashi da son wasan kwallon kafa sosai. Ga shi har girma ya zo amma abin yana jikina.

Ina iya tunawa tun muna yara idan aka dora mana talla sai mu tafi da kayan tallar wajen kwallon kafa ba tare da damuwar na sayar ko ban sayar ba.

Sai ya zamana ma da yamma duk abin da nake yi, to zan bar shi in tafi filin wasa.

Da zarar karfe hudu ta yi maigidana ma ya sani zan yi sallama da shi in tafi filin kwallo.

Tun ana hana ni a gida har aka gaji aka hakura.

Tun muna yin wasa a makaranta sai ga shi mun zo muna yi a unguwa. Muka zo kuma muna wakiltar karamar hukumarmu ta Fagge.

Muka dawo muna bugawa a matakin jiha yanzu kuma ga shi muna bugawa a matakin kasa.

Wadanne kulob-kulob ka buga wa wasa?

Da farko na buga wa kulob din Soccer Boys sai na buga wa Zumunta daga nan na buga wa Junior Fancy sai Soccer Striker.

Daga bisani sai na tafi Bank of the North, sai kuma na koma kulob din Jihar Zamfara sai Jihar Nasarawa daga nan sai na dawo Kano wato Kungiyar Kano Pillars.

Mene ne sirrin dadewarka a wasan kwallon kafa?

Yin wasa. Ni a gaskiya inda ina da lafiya ba na yarda in zauna ba na buga wasa.

Domin akwai wadansu ’yan wasa da idan suka ga kungiyarsu za a yi doguwar tafiya, sai mutum ya kirkiri wata cuta ya laka wa kansa don kada ya je ya buga wasa.

Wane dan wasa kake koyi da shi?

Gaskiya ba wani ba ne illa Cristiano Ranoldo.

Duk da yake ana ganinka a matsayin fitaccen dan wasa da ake cewa ka zura kwallo 100 a raga, ka gamsu da ci gaba da zama a Najeriya?

To kin san rayuwa komai Allah ne Yake yi. Ita harkar kwallon kafa idan Allah Ya yi za ka yi sai ka yi.

Gaskiya ne ban gamsu da zaman da nake yi a nan gida ina buga wasa ba domin koyaushe ina addu’a Allah Ya zaba min abin da ya fi alheri a gare ni.

Daukakar da na samu na san Allah ne Ya ba ni, ba wai wayo ko karfina ba don idan tsayawa za a yi a yi lissafi, to na san kwallon da na ci sun fi 100. Wannan baiwa ce daga Allah. Alhamdulillah.

Ana ganin cewa ba a yi maka adalci ba rashin sanya ka a ’yan wasan Super Eagles me za ka ce?

Alhamdulillah. Ni fa na yarda komai yin Allah ne. Idan Allah Ya nufa za a kira ni, to na san sai hakan ta kasance.

Haka idan Alalh bai yarda ba, hakan ba za ta kasance ba.

Ministan Wasanni Sunday Dare ya ce kocin Super Eagles ya rika sanya ’yan wasan cikin gida yaya kake kallon wannan batu?

Wannan shawara ce mai kyau domin ina da yakinin cewa ’yan kwallon kasar nan za su yi duk abin da ake bukata.

Domin yaran nan da kake gani suna da duk abin da ake nema a wurin ’yan wasa dama ce kawai da ba su samu ba.

Yaya kake kallon gasar Firimiyar Najeriya?

A gaskiya ana kokari sai dai akwai bukatar a kara kokari. Wani abu da na lura yana kawo ci baya a harkar shi ne dagedagen lokacin wasan da ake yi. Za a sa lokaci daga baya sai a zo a daga.

Wannan ba abu ne mai kyau ba. Idan muka gyara sai ka ga abubuwanmu sun yi kyau.

Kana tunanin za ku iya samun nasara a Firimiyar Najeriya?

Ni fa har yanzu ban fid da tsammani ba, domin na san Allah ne Mai yi kuma muna nan muna addu’a kuma mun san Allah Mai jin rokon bayinSa ne.

Idan Allah Ya sa muka samu nasara a waje, muka kuma ci gaba a hakan to za mu iya samun akalla nasara biyu a waje, da ma watakaila kunnen doki daya.

Yaya kake kallon dawowar Ahmed Musa zuwa Kano Pillars?

Wannan abu da ya yi ya dace sosai. Hakan yana sa gasar ta kara karfi sosai.

Domin ko a Turai ma za ka ga ’yan wasa suna komawa kulob dinsu na gida suna wasa.

Ba wai dan wasa ya rika jin cewa shi fa ya fi karfin ya buga wa wani karamin kulob wasa ba.

Wane kira kake da shi ga ’yan uwanka ’yan kwallo?

Ina kira gare su da su daure su rika buga wasa a duk lokacin da kulob dinsu zai yi wasa.

Su kuma rika motsa jiki a koyaushe, domin motsa jiki shi yake kara wa dan wasa lafiya yadda zai samu damar yin wasa cikin lafiya da kuzari.