✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu Jonathan bai shiga jam’iyyarmu ba — Shugaban APC na Bayelsa

Sai dai jam’iyyar ta ce yana da ’yancin shigarta idan yana da sha'awa

Shugaban jam’iyyar APC a Jihar Bayelsa, Dokta Dennis Otiotio, ya ce har tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan bai shiga jam’iyyar su ba.

Sai dai Shugaban jam’iyyar ya ce Jonathan din na da ’yancin shigata a duk lokacin da ya ga dama.

Dennis ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta wayar salula ranar Talata.

Yana tsokaci ne kan yunkurin da wasu ke yi na ganin tsohon Shugaban Kasar ya fito takara a jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

Ya ce, “Tsohon Shugaban Kasa har yanzu bai yi rajista da APC ba. Amma yana da ’yancin yin haka.

“A shirye muke mu karbe shi, a matsayinmu na jam’iyya, babban burinmu shi ne mu lashe zabe, hanyar kawai da za mu iya yin hakan cikin sauki ita ce ta karbar karin mutane a cikinmu,” inji Dokta Dennis.

A ranar Litinin ce dai wata kungiya ta saya wa tsohon Shugaban fom din tsayawa takarar a karkashin jam’iyyar APC.

Sai dai Jonathan, ta bakin mai magana da yawun shi, Ikechukwu Eze, a ranar Litinin, ya nesanta kan shi daga takarar, inda ya ce ba da yawun shi aka sayi fom din ba.

A kan haka ne ya yi watsi da fom inda ya ce a kai kasuwa. (NAN)