✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harbe-harbe a Aso Rock: Doka za ta yi aikinta —Buhari

Shugaba Buhari ya ce doka za ta hau kan duk wanda ke da hannu a harbe-harben da aka yi a Fadar Shugaban Kasa ta Aso…

Shugaba Buhari ya ce doka za ta hau kan duk wanda ke da hannu a harbe-harben da aka yi a Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock.

‘Yan sanda masu tsaron Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari sun bude wuta a fadar gwamnati a lokacin da take sa-in-sa da wani ma’aikaci kuma dan uwan Buharin, Sabiu Tunde Yusuf.

Hadimin Shugaban Kasa kan Yada Labarai Garba Shehu ya ce Buhari ya umarci a yi bincike tare da hukunta masu laifi yadda doka ta tanada.

Sai dai ya ce sabanin rade-radi, harbe-harben babu wata barazana ta lafiya ko tsaro da suka haifar wa Shugaba Buhari, kuma an yi su ne ba a gidan da Shugaban ke zama ba.

Yadda aka yi harbin

An yi harbe-harben bayan zuwan A’isha Buhari gidan Sabiu Tunde inda ta nemi ya killace kansa don gudun yada cutar COVID-19.

Rahotanni sun ce an zargi Sabiun ne da kin killace kansa bayan dawowarsa daga Legas, amma ya ce wa Aisha Shugaba Buhari ne ya ce masa babu bukatar hakan.

Bayan muhawarar ta yi zafi ne ‘yan sandan da suka rako A’isha Buhari suka fara harbi a iska, lamarin da ya sa Sabiu Tunde ya haura katanga ya tsere, a cewar rahotanni.

Daga bisani Babban Sufetan ‘Yan Sanda Mohammed Adamu ya umarci a tsare dukkan jami’an ‘yan sanda da ke tsaron lafiyar Aisha Buhari ciki har da Babban Dogarinta, Usman Shugaba.

Aisha Buhari ta jawo cece-ku-ce

Bayan haka ne A’isha Buhari ta shafinta na Twitter ta bukaci Sufeta Janar din ya sako masu tsaron lafiyan nata da aka tsare.

Hakan ya haifar da cece-ku-ce tare da kirayen a gudanar da bincike tare da zartas da hukunci.

PDP ta bukaci Majalisa ta kai dauki

Jam’iyyar PDP a cikin wata sanarwa ta bukaci Majalisar Tarayya shiga tsakani a rikicin na Fadar Gwamnati.

Kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya zargi masu kula da Fadar Gwamnatin da gazawa wurin tabbatar ta tsari domin bayar da shugabanci na gari.

Martanin da gwamnati ta bayar

Sai dai a martaninsa, Garba Shehu ya ce maganganun da ake yadawa cewa an yi barazaga ga rayuwar Shugaba Buhari ba na kamawa ba ne.

“Rayuwar Shugaba Muhammadu Buhari… ba ta fuskanci wata barazanar tsaro ko ta lafiya ba sakamakon abin da jami’an tsaron da ke tsare ana bincikensu suka aikata.

“Abin da ake magana ya faru ne ba a cikin gidan da Shugaban Kasa ke zama ba.

“Jami’an tsaron da ke aiki a Fadar Shugaban Kasa na da horon da ya dace musamman na sarrafa makamai. Idan kuma suka gaza, hukummin da abin ya shafa na da dokokinsu na magance su nan take.

“Umurnin da Shugaban Kasa cewa a yi cikakken bincike ya yi daidai da tanadin doka.

“Game da abin da ya faru kuwa, Shugaban Kasa ya ce a bar doka ta yi aikinta”, inji Sanarwar.