✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harbin Lekki: Fashola ya gano boyayyar kyamara

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya gano wata boyayyar kyamara a inda aka yi harbe-harbe lokacin zanga-zangar #EndSARS a Lekki. Fashola ya gano ta…

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya gano wata boyayyar kyamara a inda aka yi harbe-harbe lokacin zanga-zangar #EndSARS a Lekki.

Fashola ya gano ta ne a lokacin da ya jagoranci wakilan Gwamnatin Tarayya da Shugaba Buhari ya tura domin jajanta wa, Gwamna Babajide Sanwo-Olu, kan kashe-kashe da asarar da aka yi a Legas cikin makon da ya gabata.

“Ina tunanin za ta taimaka wajen binciken da ake yi kan harbe-harben da aka yi a Lekki.

“Akwai bukatar a tantance, a yi binciken cikin kimiya da fasaha, domin gano ainahin abin da ya faru a harbe-harben Lekki”, inji Fashola.

Fashola, wanda tsohon Gwamnan Jihar Legas ne, ya zargi cewar wasu suka dasa kyamarar kafin faruwar lamarin da wata boyayyar manufa.

Wakilan Gwamnatin Tarayyar da suka kai ziyarar sun hada da Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola; Ma’adanai, Olamilekan Adegbite; Masana’antu, Niyi Adebayo; da ministan Lafiya, Olorunnibe Mamora.

Sai kuma Gwamnonin Kudu maso Yamma, da suka hada da na Ekiti, Ondo da Oyo da kuma Legas.