✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hare-hare sun yi ajalin fiye da mutum 20 a Yemen

Hakan na zuwa ne bayan fararen hula akalla 26 sun rasa rayukansu ranar Asabar.

Mutum sama da ashirin ne suka rasa rayukansu a sakamakon wasu jerin hare-hare da ake zargin mayakan Houthi da kai wa, kan wani masallaci da kuma wata makarantar Islamiyya a Yemen.

Hare-haren sun rutsa da fararen hula, ciki har da mata da kananan yara, sun kuma raunata wasu da dama a yayin da ake fargabar karuwar alkaluman mamatan saboda tsananin da wadanda suka ji raunin ke ciki.

Kawo yanzu dai, babu wanda ya dauki alhakin kai harin da gwamnatin kasar ta ce na ta’addanci ne kuma ta dora alhakinsa  kan mayakan na Houthi.

Hakan na zuwa ne bayan fararen hula akalla 26 sun rasa rayukansu ranar Asabar a wani hari da ake kyautata zaton na bam ne da aka kai kusa da filin jirgin saman Aden, hedkwatar gwamnatin Yeman ta wucin gadi kamar yadda wani babban jami’in tsaro ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP.

Fashewar na zuwa ne kusan makwanni uku bayan kashe mutane shida a wani harin bam din da aka kai da wata mota kan tawagar gwamnan Aden wanda ya tsallake rijiya da baya.

Shi ma dai har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin harin na ranar Asabar, wanda shi ne mafi muni tun watan Disambar bara, lokacin da aka kaiwa mambobin majalisar ministocin kasar harin bam a filin jiragen saman birnin na Aden.

A cikin ’yan makwannin da suka gabata dai, fada ya yi kamari a birnin Marib mai arzikin man fetur dake yankin arewacin kasar da ya rage a hannun gwamnati.

Tun bayan barkewar rikici a tsakanin mayakan da ke adawa da gwamnatin Yemen, shekaru sama da bakwai da suka gabata, mutum sama da dubu dari suka rasa rayukansu inda miliyoyin ’yan kasar suka shiga cikin yanayi na tsananin bukatar taimako.