✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hare-haren masu jihadi sun addabi gwamnatin soji a Burkina Faso

Wannan hari shi ne mafi muni tun bayan da Kanal Damiba ya karbe ragamar mulki a kasar.

Gwamnatin mulkin soji ta Burkina Faso na fuskantar tashin hankali mafi muni na masu jihadi bayan wasu hare-haren da ’yan ta’addar suka kai.

Wannan lamari dai ya ci gaba da ta’azzara tun bayan da sojojin suka karbi mulki a cikin watan Janairun da ya gabata.

Fararen hula 23 da jami’an tsaro 13 ne suka mutu a wasu jerin hare-hare guda hudu a cikin ’yan kwanakin nan a yankin Dori, daya daga cikin manyan garuruwan Arewa maso Gabashin kasar.

’Yan gudun hijirar Burkina Faso a wani sansani a Tougbo

Gidan Rediyon Jamus ya ruwaito cewa wannan hari shi ne mafi muni tun bayan da Kanal Paul-Henri Sadaogo Damibaya karbe ragamar mulki a kasar.

A cikin watan Faibrairun da ya gabata ne Kanal Damiban ya hambarar da gwamnatin Shugaba Roch Marc Christian Kaboré a kan dalilan gaza magance matsalar rashin tsaro.