✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hari kan tashar jirgin kasa ya hallaka kusan mutum 40 a Ukraine

Sai dai Rasha ta ce sam ba ita ta kai harin ba

Akalla mutum 39 sun mutu, wasu da dama kuma sun jikkata, sakamakon wani hari da aka kai kan tashar jirgin kasa ta birnin Kramatorsk da ke Gabashin Ukraine.

Gwamnan yankin Donetsk da ke kasar ya ce dubban mutane ne kuma ke kokarin tserewa daga tashar bayan harin da suka zarti kasar Rasha da kai wa kan tashar.

Rasha dai ta mamaye Ukraine ne a watan Fabrairun da ya gabata, sannan duk wani yunkurin tattaunawa tsakanin kasashen biyu ya ci tura.

Sai dai Rashar ta nesanta kanta daga harin, inda Kakakin gwamnatin kasar ya ce sam ba su kaddamar da hari a yankin ba.

Bisa ga dukkan alamu dai Rasha na dada matsa lamba ne wajen kutsawa yankin Donbas da ke Gabashin kasar, yayin da take janyewa daga Arewaci, sannu a hankali.

Biranen da ke yankin na Donbas dai sun fuskanci hare-hare cikin dare daga Rasha, yayin da mutane ke ficewa don neman mafaka.

Sai dai Firaministan Birtaniya, Boris Johnson zai tattauna da Shugabar Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, kuma ana sa ran su gudanar da wani taron manema labarai na hadin gwiwa daga bisani.

Tuni dai Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai, Ursula Von der Leyen ya tafi birnin Kyiv don tattaunawa da Shugaban Ukraine, Volodimir Zolenskyy.