Harin bam ya kashe mutum 25 a Afghanistan | Aminiya

Harin bam ya kashe mutum 25 a Afghanistan

Wata motar daukar marasa lafiya yayin da ‘yan Taliban ke daukar matakan tsaro bayan da wani asibitin sojoji da ke yankin Wazir Akbar Khan ya fuskanci tagwayen bama-bamai a Kabul babban birnin kasar Afghanistan, a ranar 2 ga Nuwamba, 2021.
Hoto daga Andalou
Wata motar daukar marasa lafiya yayin da ‘yan Taliban ke daukar matakan tsaro bayan da wani asibitin sojoji da ke yankin Wazir Akbar Khan ya fuskanci tagwayen bama-bamai a Kabul babban birnin kasar Afghanistan, a ranar 2 ga Nuwamba, 2021. Hoto daga Andalou
    Ishaq Isma’il Musa

Kimanin mutum 25 ne suka mutu sannan gommai suka jikkata, sakamakon wani hari da aka kai asibitin sojoji da ke Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.

An fara kai harin ne a lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a kusa da kofar shiga asibitin Sardar Daud Khan, inda daga bisani wasu dauke da bindigogi suka shiga harabar asibitin tare da yin harbi kan mai uwa da wabi.

Tuni dai Taliban ta dora alhakin kaddamar da wannan sabon hari a kan kungiyar IS, inda wani mai magana da yawunta, Bilal Karimi, ya shaida wa BBC cewa mayakan kungiyar IS sun shiga harabar asibitin, tare da dasa bam na farko a daidai kofar shiga.

Mista Karimi ya kara da cewa su ma mayakan Taliban sun maida martani ta hanyar budewa daya daga cikin maharan wuta da cafke guda a raye.

Haka kuma babban Mai Magana da Yawun Taliban, Zabihullah Mujahid, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mayakan Taliban na musamman da jirgi mai saukar ungulu ya sauke mayaka inda suka hana maharan shiga cikin asibitin.

Ko a bayan nan Kungiyar IS ta dauki alhakin kai munanan hare-hare guda hudu tun bayan da Kungiyar Taliban ta karbe iko a ranar 15 ga watan Agusta, ciki har da harin kunar bakin wake da aka kai kan masallatan ’yan Shi’a da IS din ke musu kallon ’yan bidi’a.

Taliban ta shafe sama da shekaru 20 tana gwabza fada da hambararriyar gwamnatin da Amurka ke marawa baya,

Sai dai abin da bayanai ke cewa shi ne, a yanzu gwamnatin Taliban na fafutikar samar da zaman lafiya a Afganistan, wadda a cikin ’yan makonnin da suka gabata ta fuskanci hare-haren wuce gona da iri da kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa.