✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin bom ya hallaka mutum 12 a filin jirgin Yemen

Bom din ya tashi ne a lokacin da jami’an sabuwar gwamnatin kasar ke sauka daga Saudiyya.

Akalla mutane 12 ne suka mutu bayan wani mummunan harin bom da harbe-harbe a filin jiragen sama na birnin Aden a kasar Yemen ranar Laraba.

Harin dai ya faru ne a daidai lokacin da jami’an sabuwar gwamnatin rikon kwaryar kasar ke sauka a filin daga Saudiyya.

Wasu majiyoyi a gwamnatin kasar sun shaida wa jaridar The Independent cewa akalla mutum 12 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, ciki har da Mataimakin Ministan kasar.

Bom na farko da ya fara tashi, gidan Talabijin na Al-Hadath ya nuna yadda hayaki na turnuke mafitar filin jirgin, a daidai lokacin da jami’an gwamnatin ke sauka daga jirgi.

Daga bisani kuma an hangi daruruwan jami’an tsaro, ma’aikatan filin jirgin da ma ’yan kallo na kokarin guduwa domin tsira da rayuwar su.

Daga nan ne kuma aka biyo harin da wasu harbe-harbe da wasu kananan fashe-fashe wanda wasu kafafen watsa labaran kasar suka bayyana da cewa gurnetoci ne da nakiyoyi ne.

Jami’an sabuwar gwamnatin wadanda suka hada da Firaminista Maeen Abdulmalik sun sauka ne zuwa sabuwar Fadar Shugabn Kasar, kamar yadda mataimakin Ministan Matasa da Wasanni, Hamza al-Kamaly ya ce.

Hamza ya kuma ce mataimakin Ministan Sufurin kasar da ma wasu shugabannin al’umma da fararen hula da dama sun ji raunuka.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, ko da yake Hamza ya ce hukumomin kasar na zargin kungiyar ’yan tawayen Houthi wacce Iran take goya wa baya ce ta kai shi.

’Yan tawayen Houthi wadanda a yanzu haka ita ke iko da Arewacin Kasar ta shafe kimanin shekara biyar tana fafatawa da gwamnatin kasar ta Yemen.

Wasu hotunan da The Independent ta wallafa sun nuna gawarwakin wasu daga cikin wadanda harin ya ritsa da su sun yi dai-dai a kan hanya, yayin da gilasai da karafa suka farfashe a jikin gine-ginen da harin ya lalata.