✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai wa masu sayayyar Babbar Sallah harin bom a kasuwa

Bom ya yi gunduwa-gunduwa da mutum 35 mutane ya kuma cire rufin gine-gine.

Akalla mutum 35 ne suka mutu a wani harin bom a wata kasuwa a yayin da Musulmi ke tsaka da sayayya a ranar jajibirin Babbar Sallah.

Harin kunar bakin waken a yankin Sadr da ke Gabashin Bagadaza, babban birnin kasar Iraqi ya yi gunduwa-gunduwa da mutane tare da jikkata akalla wasu mutum 50 a kasuwar.

Wani bidiyo da aka wallafa a dandalin sadar da zumunta ya nuna mutane jina-jina suna koke-koke tare da neman dauki bayan tashin bom din da ya cire rufe wasu gine-gine.

“An kai harin a Kasuwar Woheilat da ke yankin Sadr ta hanyar amfani da abun fashewa, inda mutane da dama suka rasu, wasu kuma suka samu raunuka,” a cewar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Iraki.

Kungiyar IS ta ce wani mayakinta ne ya kai harin ta hanyar tayar tayar da bom a tsakiyar mutanen da ke cin kasuwar a daren Sallah.

Jami’an lafiya sun ce mata takwas da kananan yara bakwai na daga cikin mutanen da suka rasu a harin da aka kai a lokacin da mutane ke ta tsaka da kai-komo a kasuwar da ke birnin Sadr.

Da yake mika sakon ta’aziyyarsa kan harin na garin Sadr inda ’yan Shi’a ke da rinjaye, Shugaban Kasar Iraki, Barham Salih ya la’ance harin a matsayin tsabar rashin imani.

“Sun kai wa fararen hula a birnin Sadr a jajibirin Sallah, sun hana mutane farin ciki,” inji sakon da Shugaban Kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Rundunar tsaron hadin gwiwar Iraki ta ce ta kaddamar da bincike kan harin na daren Babbar Sallah wanda daya ne daga cikin hare-hare mafi muni a cikin shekara ukun da suka gabata.

A watan Janairu, kungiyar IS ta yi ikirarin kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 32 a wata kasuwa mai cunkoson jama’a a birnin Bagadaza.

Ana yawa samun irin wadannan hare-hare a Bagadaza, tun bayan da Amurka ta fara mamaye kasar a shekarar 2003, bayan kifar da gwamnatin Shugaba Saddam Hussain.