✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Filato: An gano gawawwaki 50, gidaje fiye da 100 sun kone

Wasu bayanai na cewa an kashe mutum 135 yayin hare-haren.

Fiye da gawawwakin mutane 50 aka gano a kauyukan Karamar Hukumar Kanam da ke Jihar Filato.

Wannan na zuwa ne biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka hudu a ranar Lahadin da ta gabata.

Aminiya ta ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan Kukawa, Gyanbahu, Dungur da Keram inda suka kashe gomman mutane sannan suka kone gidaje fiye da 100 kamar yadda ganau suka tabbatar.

Maharan sun kai farmakin ne haye a kan babura, inda suka dinga harbe mutane suka kuma sace shanu

Mazauna yankin sun kuma bayyana cewa an kwashe kusan kwana guda kafin jami’an tsaro su kai musu dauki.

Sun kara da cewa wadannan su ne hare-hare mafiya muni da aka taba kai wa a yankin.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Filato, ASP Ubah Gabriel ya ce sun tura karin jami’an tsaro a yankin, sai dai bai yi wani cikakken bayani daga haka ba.

Wani mazauni a daya daga cikin kauyukan da abin ya shafa, Adam Musa, ya shaida wa Aminiya cewa an gano gawawwaki 24 a kauyen Kukawa, 15 a Gyanbahu da wasu takwas a Dungur sai karin wasu hudu a kauyen Keram.

Ya kara da cewa, wadanda suka jikkata an mika su asibitoci daban-daban ciki har da Babban Asibitin Dangi da ke Karamar Hukumar Kanam ta jihar.

Wasu bayanai na cewa an kashe mutum 135 yayin hare-hare da ’yan bindiga suka kai.

Wani basaraken gargajiya a yankin ya shaida wa BBC cewa tuni aka gano gawar mutum 54 a kauyen Kukawa da kuma gawar mutum 34 a kauyen Gyambau.

Jihar Filato dai ta sha fama da rikice-rikice da ke da nasaba da kabilanci da kuma addini, amma a baya-bayan nan ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa sun ta’azzara matsalar.