✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin Gaza ya hallaka mutum 120 ya jikkata 830

Isra’ila ta ci gaba da luguden wuta a kan Gaza a matsayin martani ga hare-haren Hamas.

Isra’ila ta ci gaba da luguden wuta a kan Gaza a matsayin martani ga hare-haren da mayakan Hamas ke tsananta kaiwa da rokoki da manya-manyan bindigogi a kan yankunan Yahudawa.

Lamarin da ya yi sanadin rasa rayukam mutane sama da 120, a Gaza.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce hare-haren da ta kaddamar cikin dare sun hada da na jiragen yaki da tankuna a kan wata hanyar bututun karkashin kasa da Hamas ta gina a yankunan fararen hula.

Sai dai ta ce a wannan karon ba ta samu damar ankarar da fararen hula kamar yadda ta yi gabanin hare-haren da ta yi a a satin da ya wuce ba.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, ya ruwaito cewa gidaje da dama a yankunan Gaza da ke da yawan jama’a sun salwanta.

Ministan Lafiyar Gaza, ya ce rayukan Falasdinawa 119 ciki har da yara 31ne suka salwanta, sannan 830 suka samu rauni.

Wata mata, Bayahudiya, wacce ta zarce shekaru 80 da haihuwa ta rasu a cikin daren Alhamis sakamakon raunukan da ta samu a yayin da take neman mafaka daga rokokin da ake harbawa, abin da ya kawo adadin mamata a bangaren Isra’ila 8, ciki har da wani yaro mai shekaru 6, da soja daya.

Sama da rokoki 1,800 ne mayakan Hamas suka harba wa Isra’ila, akasari a biranen Kudancin kasar, ciki har da Tel Aviv da birnin Kudus.