✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Gidan Yarin Kuje: An kama fursuna daya a wata tashar mota a Abuja

An cafke fursunan da kulli uku na tabar wiwi yana shirin tafiya Maiduguri.

Daya daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja a makon jiya ya shiga hannu.

Fursunan mai suna Suleiman Idi, ya fada komar jami’an tsaron Hukumar Hana da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a wata tashar mota da ke babban birnin kasar yana shirin tafiya Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Aminiya ta ruwaito yadda wasu ’yan bindiga suka kai hari gidan gyara halin na Kuje inda suka kubutar da daruruwan fursunoni ciki har da ’yan ta’addan Boko Haram.

Tun bayan kai harin ne Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali ta Najeriya NCoS, ta fitar da sunaye da fuskokin ’yan ta’adda 69 daga cikin fursunonin da take nema ruwa a jallo.

Binciken Aminiya ya gano cewa, fursunan da ya shiga hannu shi ne na hudu a jerin sunayen fursunonin da Hukumar NCoS din ke nema ruwa a jallo.

An dai kama Suleiman Idi da kulli uku na tabar wiwi a tashar mota ta Area 1 da ke Abuja.

Da yake yaba wa kwazon jami’ansa, Shugaban Hukumar NDLEA Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya umarci a gaggauta mika wa Hukumar NCoS fursunan.

Suleiman Idi shi ne fursuna na biyu da aka kama daga cikin fursunonin 69 da Hukumar NCoS ke nema ruwa jallo.

A ranar Asabar da ta gabata ce aka cafke Hassan Hassan a Jihar Nasarawa kamar yadda mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Rahman Nansel ya tabbatar.