✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin Giwa: Wadanda suka mutu sun karu zuwa 40

An samu karin gawar mutum biyu bayan wani bincike da jami'an tsaro suka gudanar.

Adadin wadanda suka mutu a harin da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka a Jihar Kaduna a karshen mako ya karu zuwa mutum 40, bayan samun karin gawar mutum biyu da aka yi.
Kwamishinan Tsaron da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a ranar Litinin, cikin wata sanarwa.
“Karin gawar mutum biyu da aka samu ya sa adadin wanda suka mutu karuwa zuwa 40. Za a fitar da karin bayani da zarar an tabbatar da komai,” inji Aruwan.

A cewarsa, jami’an tsaro sun gudanar da bincike a yankunan da abin ya shafa inda aka samu karin gawar mutum biyu.

Aminiya ta rawaito yadda mahara suka kai farmaki kauyukan Kauran Fawa, Marke da Riheya a mazabar Idaso da ke Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, a ranar Lahadi, suka kashe mutum 38.