✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Imo: Fursunoni 40 sun koma gidan yarin Owerri

Fursunonin sun dawo bayan alkawarin yafe musu laifin tserewa da Minista Aregbesola ya yi.

An samu karin akalla fursunoni 40 da suka koma gidan gyara hali da ke babban birnin Jihar Imo bayan tserewarsu.

Ya zuwa ranar Laraba, adadin fursunoni 82 ne suka koma gidan gyara halin da ke Owerri.

Fursunoni fiye da 1800 ne suka tsere bayan wasu bata gari sun fasa gidan yarin a ranar Litinin.

Aminiya ta ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga ne suka kai hari shelkwatar ‘yan sanda da ke Jihar tare da kone sashen da ake ajiye bayanan manyan laifuka, sannan suka saki wasu da ke daure.

Yayin ziyarar gani da ido kan ta’asar da Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya kai a ranar Talata, ya ce za a yafe wa duk fursunan da ya dawo gidan yarin don kansa.

A wata tattaunawa da Aminiya ta yi da Kakakin Hukumar Kula da Fursunonin Jihar Imo, Mista Joe Madugba, ya ce fursunonin sun fara dawo gidan yarin ne daga ranar Talata zuwa Laraba.

Kazalika, Mista Madugba ya ce suna sa ran wasu da dama za su iya dawowa gidan yarin.