✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Isra’ila ya rusa ofishin gidan talabijin na Al-Jazeera

Isra'ila ta kashe mutum 10 ’yan gida daya a sansanin gudun hijira da ke Gaza.

Isra’ila ta harba makami mai linzami a kan ofishin gidan talabijin na AlJazeera da kamfanin dillancin labarai na AP da wasu kamfanonin jarida da ke cikin birnin Gaza.

Isra’ila ta kuma kashe mutum 10, cikinsu har da kananan yara takwas, da mata biyu duk ’yan gida daya a harin da ta kai a sansanin ’yan gudun hijira a Gaza.

Bidiyon harin da gidan talabijin na Alarabiya ya dauka, an ga yadda makami mai linzami da Isra’ila ta harba ya rusa katafaren benen har kasa.

Mai ginin benen, Jawwad Mahdi, ya bayyana cewa hukumar Sojin Isra’ila ta kira shi cewa za a kai wa gidansa hari.

Ya bayyana cewa an fada masa ya sanar da wadanda ke cikin ginin su tattara kayansu su bar ginin cikin awa daya.

Daga ranar Litinin zuwa yanzu, kungiyar Hamas ta harba rokoki akalla 2,000 kan Isra’ila, sai dai rundunar sojin kasar ta ce ta kakkabo wasu daga cikin rokoki.