Akalla mutum 68 rahotanni ke cewa na hannun ‘yan bindigar da suka kai hari jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.
Wani bidiyo da aka fitar wanda ya rinka yawo har a kafofin sada zumunta, na tabbatar da cewa ‘yan bindigar na rike da mata 41 da maza 22, sai kuma yara biyar.
- Majalisar Dokokin Pakistan ta zabi jagoran ’yan adawa sabon Firaminista
- Mourinho ya nemi afuwar Salernitana
Wannan na zuwa ne mako biyu bayan kai kazamin harin bam a jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, mutane da dama sun rasa rayukansu baya ga wadanda aka jikkata.
Mako guda bayan harin hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen kasa a Najeriya ta fitar da sanarwar da ke cewa har yanzu akwai fasinjoji 146 da ba a ji duriyarsu ba.
Sai dai shugaban Bankin Manoma, Mallam Alwan Hassan, da ya samu kubuta a makon da ya gabata shi ya ba da alkaluman mutanen da ke hannun ‘yan bindigar a lokacin da ya ke bayani kan halin da ya tsinci kansa.
Bayan kai harin, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce sun san da cewa za a kai harin, sannan ya shaida cewa dama mayakan Boko Haram yanzu na cin karensu babu babbaka a dazukan yankunan Kaduna har zuwa Neja.