✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Kaduna: Tinubu ya ba da tallafin miliyan 50

Tinubu ya kai ziyarar ce don jajanta wa Jihar kan harin bam da ’yan bindiga suka kai

Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a APC, Bola Tinubu, ya ba mutanen da hatsarin jirgin kasan Kaduna ya shafa gudunmawar Naira miliyan 50.

Tinubu ya ba da tallafin ne lokacin da yavkai ziyarar jaje Jihar ga Gwamna Nasir El-Rufai tare da Jajanta wa daukacin jama’ar Jihar bisa harin.

Dan takarar dai ya samu rakiyar tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, yayin ziyarar.

Ya samu tarba daga Gwamna El-Rufai da Sanata Uba Sani da Sanata Suleiman Abdu-Kwari a gidan gwamnatin jihar Kaduna.

Sauran ’yan tawagar ta Tinubu sun hada da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da Sanata Abu Ibrahim.

Tinubu ya bayyana harin jirgin kasa a matsayin wani bala’i da ya shafi kasa baki daya.

A cewarsa, ya kamata kowa ya damu da hare-haren da ke faruwa a jihar Kaduna wanda ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.

Da yake jawabi, El-Rufai ya gode wa Tinubu kan yadda ya nuna goyon bayansa ga al’ummar Jihar Kaduna kan harin da aka kai ta hanyar soke taron bikin zagayowar ranar haihuwarsa domin nuna alhininsa ga wadanda suka rasa rayukansu.

Ya kuma gode wa Tinubu bisa jajircewarsa ta ganin an samu hadin kai da ci gaban Najeriya.

El-Rufai, ya ce yana sane da burin Tinubu na son zama Shugaban Kasa, ya kara da cewa a halin yanzu Najeriya ta shiga tsaka mai wuya, kuma dole ne a dauki matakin da ya dace ta kowane hali.