✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Kuje: An kara samun wani fursuna a Katsina

Fursunan da aka samu da kayan masu cin sarka ya ce tsintar su ya yi a juji.

An kuma samun daya daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan gyaran hali na Kuje da ya shiga a hannu a Karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina.

Tserarren fursunan Abdulkadir Musa mai shekaru 30, ya shiga hannun jami’an ’yan sanda a garin Bakori a ranar Juma’ar nan.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Abdulkadir Musa ya shiga hannu yayin wani bincike da jami’an ’yan sandan ke gudunarwa.

Fursunan wanda aka kama da kayan masu cin sarka ya ce a juji ya tsinta saboda shi dan jari-bola ne.

Abdulkadir shi ne tserarren fursuna na biyu da aka kama a wannan Juma’ar a Jihar Katsina, inda wani mai suna Kamala Abubakar ya riga shi shiga hannu a Karamar Hukumar Danmusa ta jihar.

Ya zuwa yanzu dai an cafke wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan gyara hali na Kuje da ke Abuja, babban birnin kasar

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 5 ga watan Yuli ne wasu ’yan bindiga suka far wa gidan yarin na Kuje da ke babban birnin kasar, inda suka kubutar da mutane da dama, ciki har da fursunonin da ake zargin mayakan Boko Haram ne, wadanda ake tsare da su.

Tun bayan kai harin ne Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali ta Najeriya (NCoS), ta fitar da sunaye da fuskokin ’yan ta’adda 69 daga cikin fursunonin da take nema ruwa a jallo.