✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Rasha: Shi ne mafi girma tun bayan Yakin Duniya na II

Wannan shi ne yaki mafi muni tun bayan yakin duniya na II.

Sa’o’i kalilan bayan yakin da ta kaddamar a kan Ukraine, Rashan ta sanar da lalata cibiyoyin sojin Ukraine sama da 70, ciki har da filayen saukar jiragen sama 11.

A nata bangaren, rundunar sojin Ukraine ta ce dakarunta sun samu nasarar kashe sojojin Rasha kusan 50  tare da lalata jiragen yakinta shida, yayin barin wutar da kasashen biyu ke yi, tun ranar Alhamis.

Tuni shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar, tare da yin kira ga jama’a da su bayar da gudunmawarsu ga yakin.

Gwamnatin Ukraine ta ce fararen hula da dama sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren da Rasha ke kaiwa.

Ta kuma ce za ta bayar da makamai ga duk wanda yake da kudurin kare kasar.

An yi ittifaki cewa yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine din shi ne mafi girma da muni da aka taba gani a nahiyar Turai tun bayan Yakin Duniya na Biyu.

Kasashen Yammacin Turai sun yi Allah-wadai da matakin Rasha na kaddamar da yaki a kan Ukraine.

Fira Ministan Birtaniya, Boris Johnson, ya kira Putin a matsayin mai mulkin kama-karya, kuma ya yi gargadin cewa yanzu kasar za ta fuskanci gagarumin takunkumi daga Yammacin Turai.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres, ya roki Vladimir Putin da ya janye sojojin Rasha daga Ukraine.

A nata bangaren, Ukraine ta roki kasashen duniya da su tallafa mata wajen yakar kasar Rasha.

Yakin tsakanin kasashen biyu ya dugunzuma ilahirin duniya, inda manyan kasashe suka shiga zulumi kan abin da yakin zai haifar ga duniya baki daya.